Daga A'isha Suleiman Zariya An sami faruwar wani mummunar haÉ—arin mota a garin Lere karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna. W...
Daga A'isha Suleiman Zariya
An sami faruwar wani mummunar haÉ—arin mota a garin Lere karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.
Wakiliyarmu ta sami cikakken bayani akan yadda lamarin ya faru a satin da ya gabata.
Mummunar haɗarin ya faru ne a tsakiyar garin Lere yayin da wata babban mota Tirela ta niƙe wata mota ƙirar J5 da take ɗauke da mutane kimanin 73 a cikin motar a sanadiyar gittawar da wani mai Babur ya yi masu a tsakaninsu a cewa wanda suka ga yadda lamarin ya faru.
Lamarin kuma ya rutsa ne da mutanen garin Ƙwandari yayin da suka fito zuwa garin Saminaka taron Mauludin Fiyayyen Halitta Annabi (SAW) na bana wanda aka fara tun daga farkon watan Rabi'ul Auwal na wannan shekarar a dukkan faɗin wannan ƙasa da duniya baki ɗaya.
Sakataren ƙaramar hukumar Leren Honorabul Saifullahi Usman, Saminaka ya tabbatar da faruwar haɗarin a yayin da yake ƙarin haske ga manema labarai a gidan Sarkin garin na Kwandari lokacin da jama'ar garin suka tarbi babban malamin addinin Muslunci kuma shugaban ƙungiyar Maj'ma'ul- Ahbabul-Sheik Ibrahim Inyass na ƙasa daya ziyarce su don jajantawa.
Honorabul Saifulahi ya ce, sun gamu da if'tila'i mai girma gaske amma sun É—auki mataki na gaggawa yanzu haka.
Bincike ya tabbatar da cewa da yawan rayukan da aka rasa a haɗarin mata ne da ƙananan yara.
Kuma sun yi tafiyar ne ƙarƙashin ƙungiyar su ta Maj'ma'ul-Ahababul-Sheik Ibrahim Inyass (R) ta ƙasa reshen karamar hukumar Lere.
Bisa haka ne ƙungiyar ta ƙasa ta wakilta shugaban ta Sheikh Sharif Muhammad Dallami Zariya limamin masallaci Juma'a na Realway Sabon Gari Zariya ya je ya yi ta'aziyyar rashin da aka yi masu ga iyalan wanda suka rasa rayukansu da dangogin su da dukkan al'ummar musulmi jihar Kaduna da ƙasa baki ɗaya.
A lokacin da Sheikh ɗin ke yin hira da manema labarai a fadar Sarkin garin na Ƙwandari ya tabbatar da rasuwar mutanen 33 take kuma mutum 27 suna ƙwance a asibiti rai ga hannun Allah ya kuma nuna al'hininsa tare da kira ga gwamnati ƙaramar hukuma da na jiha har zuwa tarayya baki ɗaya dasu duba lamarin kuma su ɗau matakin tausayawa marayun da iyayen su suka rasa rayukansu a wannan haɗari.
Sheikh É—in ya yi godiya da jinjina ga dukkan wanda suka bayar da tallafin kuÉ—i da abinci ga iyalan wanda suka rasa rayukansu a wannan haÉ—arin.
Kuma ya janyo hankalin malamai da limamai da shugabanin kwamitoci akan ɗaukar mataki yayin da ake gudanar da bukukuwa don kaucewa faruwar irin wannan lamari irin, haka kuma ya yi addu'ar Allah ya jiƙan wanda duk suka rasu ya ce duk sun yi shahada ne saboda sun koma ga Allah suna murnar da haihuwar fiyayyen halitta Manzo Allah (saw).
Shima Sarkin wannan gari Malam Kabiru Dan-Asabe ya bayyana hakan a matsayin jarabawa mai girman gaske a wannan garin nasu da ƙasa baki ɗaya.
Sarkin ya kuma tabbatar da rasuwar mutane 33 take a wajan haÉ—arin yace, zuwa yanzu kuma akwai mutane 27 suna asibiti É—auke da manyan raunuka.
Ƙarshe ya yi godiya ga dukkan wanda suka bayar da taimako na nesa dana kusa kuma ya ce, sun yi tsari mai kyau don taimakawa majinyatan ta hannun lamarin garin ya kuma yi godiya ga Sheikh Sharif Muhammad Dallami, Zariya bisa kawo masu ziyara ta musamman tare da jajantawa faruwar lamarin a madadin Maj'ma'ul- Ahbabul-Sheik Ibrahim (r) na ƙasa muna godiya.
No comments