Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Raɗɗa Na Taya Ka Aiki Jiya!

Daga Dikko Muhammad Jiya da ƙarfe 2 na dare na je asibitin Turai Yar'adua. Ina nan wani mutum ya shigo da wasu mata biyu ɗau...

Daga Dikko Muhammad

Jiya da ƙarfe 2 na dare na je asibitin Turai Yar'adua. Ina nan wani mutum ya shigo da wasu mata biyu ɗauke da ƙaramar yarinya mai shekaru biyu. Sun zo tana zazzaɓi amma babu gado. Aka ce su wuce Asibitin Janaral. Amma kuma babu abin hawa. A ƙasa suka tako daga unguwar da ke bayan Gidan Rodi (Steel Rolling). Mutumin da sanda a hannunsa sai matan a bayansa. Sun ce sun fara zuwa asibitin Filin Kanada. Amma an ce masu babu ma'aikatan Lab.

Da suka ji haka, sai ɗaya daga cikin matan ta ce, "mu koma gida mu jira ikon Allah!" Tausayi ya kama ni. Na ɗauke su a mota muka tafi Asibitin Janaral saboda ina jin babu ambulance services a Turai Yar'adua.

A Janaral Hospital na gane kana da aiki Gwamna. Gaskiya sai ka tashi tsaye. Reception ɗin Ward ɗin yara cike yake tab da marasa lafiya. Wasu a kan kujeru da wasu a ƙasa kan floor. Sai kukan yara ta kowane ɓangare. Mun samu wani likita guda ɗaya, bawan Allah. Yana sanye da Lab Coat mai tambarin A.B.U Zaria.

Bayan mun yi wa Likita bayani, ya tura mu Lab aka yi PCV da sauran gwaje-gwaje. Muka je muka biya muka dawo. Sai ya ce jini yarinyar ke buƙata. Amma tunda babu space, a koma gida sai 10am a dawo. Na fara bashi haƙuri cewar daga nesa suke. Kuma har tafiyar ƙasa sun yi. Ya ce nurses na complain cewar duk ya tara masu aiki. Ni dai na ci gaba da bada haƙuri. Sai ya ce to a koma Lab a ɗauki jinin a dawo. Haka muka dawo Lab sannan na yi bankwana da su na koma Turai inda Uwargida ta haifa min Muhammad (Babangida) daidai wajen 4:30am.

To, mai girma Gwamna, tsakani da Allah aiki ya ganka. Na ga masu kwamfuta ke aikin bayar da kati da kuma payment. Amma ya kamata ka samar da ambulances a asibitoci. A faɗaɗa yawan wuraren kwantar da marasa lafiya da ƙara ma'aikata.

Ka kira 'yan majalisun tarayya su gina ko da wards biyu ne a matsayin gudummawa. Ka kira na jiha su ma. Ka kira sanatocinmu uku. Ga su Mangal da sauran masu kuɗi. Kowa ya gina ward ya sa sunansa. Suna iya zaɓen inda suke son yin wannan aikin. 

Abu na biyu kuma, ka juri yawon ziyara a asibitocin nan domin ganin haƙiƙanin gaskiya ba rahotanni daga jami'ai ba. Ka kuma yi aiki da abin da ka gani a zahiri. Ka tuna tsayuwa domin hisabi a gaban Allah inda ba lauya bare S.A ko Kwamishina ko Board Chairman.

Allah Ya ƙarfafa maka gwiwa. Allah Ya ba ka ikon aikata alkhairin da zai kwance ɗaurin da za a yi maka a lahira. Amin. 

Dikkonku,
24.09.'24.

No comments