Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga gwamnatin Neja da masu ruwa da tsaki da su dauki tsattsauran matakai kan matasan da ke anfani da mak...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga gwamnatin Neja da masu ruwa da tsaki da su dauki tsattsauran matakai kan matasan da ke anfani da makamai wajen aukawa jama'a da sunan zagayen Mauludi. Shugaban kwamitin sulhu na ma'aikatar shari'ar musulunci a jihar Neja, Sheikh Muhammadu Liman Masha'Allahu ne ya yi kiran ganin yadda wasu matasa ke fitowa da makamai suna aukawa jama'a da sunan zagayen mauludi.
Shehin malamin, ya cigaba da cewar mu da ke mauludi soyayya da shauki akan haihuwar Manzon Allah ( S. A. W) da yazo mana da shiriya yasa muke mauludi, amma ba inda a shari'ar musulunci aka amince da zubar da jinin wani balle akai ga kashe mutane, amma wasu baragurbi sun fake da zagayen mauludi suna aukawa jama'a da makamai, suna sace-sace wanda wannan ya sabawa koyarwar Manzon Allah.
Babu wani abinda za ka yi na soyayyar Manzon Allah, wanda ya sabawa karantarwar addini ya zama karbabbe, saboda haka ya kamata malamai musamman wadanda ke bada tarbiyar addini su kara kaimi da sanya idanu ga daliban su, ganin yadda aka mayar da wannan ranar tamkar ranar zubar da jini, me ya hada soyayya da tashin hankali, me ya hada soyayya da sace-sace da zubar da jinin bayin Allah.
Koda kafiri ka auka ma wa da tsoratar da shi ko ka zubar mai da jini ka sani sai Allah ya tambaye ka, balle musulmi dan uwan ka, dole iyaye da masu ruwa da tsaki suna da rawar takawa wajen kawo karshen wannan mummunar lamarin.
Jami'an tsaro kan su na cikin tashin hankali saboda lafiyarsu da rayuwarsu duk da kokarin da su ke yi, ya kamata gwamnati ta nuna da gaske ta ke yi, duk wani matashin da aka samu da makami, ko yunkurin aukawa jama'a ayi masa hukuncin da idan wani ya gani ba zai kwatanta ba.
Bai kamata a zura idanu wannan mummunar dabi'ar na cigaba ba, mun gaji mauludi shekaru da dama, amma ba mu taba ganin inda ake wannan mummunar aikin da matasan mu ke yi ba, sun mayar da wannan ranar tamkar ranar yaki wanda wannan kuskure ne babba da bai kamata a zura idanu yana cigaba da faruwa ba.
No comments