Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Me ya faru mazauna wasu sassan Abuja suka ji gidajensu sun yi motsi?

  A Æ™arshen makon da ya gabata ne dai mazauna yankunan Maitama da Katampe da Mpape a Abuja suka tsinci kansu a yanayin firgici da É—imuwa sak...

 

A ƙarshen makon da ya gabata ne dai mazauna yankunan Maitama da Katampe da Mpape a Abuja suka tsinci kansu a yanayin firgici da ɗimuwa sakamakon wata ƙara da girgiza da suka ji.

"Muna zaune da ‘ya’yana da mai aikina a falo, sai muka ji wata babbar Æ™ara kamar wani abu ya fashe sannan gidan ya É—an girgiza.

Mai gidana yana bacci a kan bene ya tashi cikin ruÉ—ani yana tambaya me ke faruwa? Nan take sai na wallafa “me ke faruwa a Maitama? a kafar sada zumunta ta snapchat.

Mutane da dama suka rubuto min cewa su ma sun ji wannan girgizar. Wata ta shaida min cewa gidanta yana unguwar Jahi amma ta ji girgizar." In ji Hajiya Fatima, wata mazauniyar unguwar Maitama a Abuja.

Satumba 2018

Wannan ne dai karo na biyu da mazauna wasu sassan babban birnin ke jin irin wannan ƙara kamar fashewa da kuma girgiza na wasu ƴan daƙiƙai.

Ko a shekarar 2018 ma an taɓa samun irin wannan yanayi na motsin ƙasa na kwana biyu, wani abu da ya ja hankalin mutanen Najeriya da ma ƙasashen waje inda kuma hukumomi suka bayar da tabbacin cewa babu wata matsala.

Al'amarin dai ya jefa razani a zukatan mazauna unguwannin inda suke ta neman bayani dangane da haƙiƙanin abin da ke faruwa a yankunan nasu.

Unguwannin Maitama da Katampe dai na maƙwabtaka da Mpape, inda ake da yawan wuraren haƙa da fasa duwatsu. Kuma wasu na alaƙanta motsin ƙasa da ƙara da mazauna yankin ke ji.

Me hukumomi suka ce?

Gwamnatin tarayya ta bakin ministan ma'aikatar Kimiyya, Fasa da Ƙirƙire-ƙirƙire, Uche Nnaji a wani taron manema labarai ranar Laraba ya shaida cewa "motsin ƙasar ba wani abin damuwa ba ne" sai dai kuma ya ƙara da cewa "gwamnati za ta ɗauki matakan daƙile sake faruwar hakan" a nan gaba.

"Gwamnati na sanya ido tare da tattara bayanai daga hukumomin da ke sa ido kan al'amarin domin miƙa wa hukumar da ke kula da babban birnin domin ɗaukar matakan da suka dace." In ji mista Uche.

Shi ma shugaban hukumar da ke kula da ƙasa da safiyo ta Najeriya, NGSA, Farfesa Olusegun Ige ya nemi mazauna yankunan da su kwantar da hankalinsu.

"Motsin ƙasar bai taka kara ya karya ba da zai iya haifar da matsala ga muhalli." In ji Farfesa, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.



No comments