Daga Idris Umar, Zariya A cikin wannan makon ne aka ƙaddamar da bikin dashen itatuwa da Alhaji Mohammed Lawal Jibirin ya ɗauki n...
Daga Idris Umar, Zariya
A cikin wannan makon ne aka ƙaddamar da bikin dashen itatuwa da Alhaji Mohammed Lawal Jibirin ya ɗauki nauyi ƙarkashin ƙungiyar cigaban garin Bomo da ke ƙaramar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.
Wakilinmu na É—aya É—aga cikin wakilan kafafen yaÉ—a labarai da suka sami halartar taron.
An gudanar da taron ne a fadar Hakimin gundumar Basawa, Alhaji Haruna Abubakar Bamalli, da ke garin Bomo.
Yayin ƙaddamar da dashen itatuwan Alhaji Lawal Jibirin ya gabatar da jawabi ga dubban jama'ar da suka sami zuwa wajen taron.
Alhaji Lawal ya fara ne da miƙa godiyar sa ga Allah maɗaukakin Sarki kuma ya jinjina wa Sarakuna da limamai da masana harkar tsirrai da suka samu halartar taron da ƙungiyoyi masu zaman kansu da suka bayar da tasu gudummawar a yankin.
Bayan haka ne ya ce maƙasudin taron shi ne ƙaddamar da dashen itatuwa a garin Bomo da kewaye.
Alhaji Lawal ya ce Itace na da mutuƙar muhimmanci ga rayuwar al'umma bisa haka Alhaji Lawal ya yi kira ga al'ummar garin Bomo da Samaru da su bayar da haɗin kai wajen shuka itatuwa a dukkan garin da ke da ɗimbin tarihi a jihar Kaduna da Nijeriya baki ɗaya.
Taron haɗin guiwa ne tsakanin ƙungiyoyi guda biyu: ƙungiyar ci gaban garin Bomo da kuma jungiyar ci gaban garin Samaru.
An gudanar da wannan taron ne a ofishin Hakimin gundumar Basawa wato Barden Kerarriyar Zazzau Alhaji Haruna Abubakar Bamalli.
Daga cikin manyan mutanen da suka gabatar da muƙaloli a wajen taron akwai wakilin shugaban Jami'ar Ahmadu Bello, Farfesa Kabiru Bala, wato Farfesa Ibrahim Jumare daga cibiyar kimiyyar tsirai ta ƙasa dake Jami'ar Ahmadu Bello Zariya wato (NAERLS)
A jawabinsa ya nuna muhimmancin dasa itace ga rayuwar ɗan Adam, ya ce itace na taimakawa lafiyar Bil'Adama a ɓangarori da dama.
Bisa haka Farfesan ya yi kira ga dukkan jama'ar da suka halarci taron da kowa ya yi ƙoƙari ya dasa itace a rayuwarsa, ya ce hakan zai sanya mutum ya sami lafiya kuma ya sami rahama daga Allah a duniya da lahira.
Shima Ɗan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar karamar hukumar Sabon Gari, Honorabul Abubakar Jamil Albani, a nasa muƙalar nuni ya yi da cewa ladan dasa itace na zama sanadi ga shiga Aljannah don haka ya yi kira ga al'ummar da suke garin Bomo da Samaru su yi koyi da addinin Musulunci wajan neman lada a sunnar dasa itatuwa a rayuwarsu.
Ahmad Muhammad Jumare (Maraɗin Zazzau) wanda shima ɗa ne a garin na Bomo a nasa jawabin ya nuna jin daɗinsa ne bisa ƙokarin da dan uwansa ya nuna na ɗaukar nauyin bikin mai muhimmanci ga rayuwar al'ummasu wato bikin dashen itatuwa a garin Bomo.
Alhaji Ahmad Jumare ya ce wannan ƙoƙari ya ƙara masu ƙaunar juna tare da karfafa zumuncinsu da ke tsakanin al'ummar garin Bomo da Samaru da sauran jama'a baki ɗaya.
Ƙarshe yayi fatan Allah ya sakawa ɗan uwan nasa da alheri mai girma a rayuwarsa har da iyalansa.
Hakimin Gundumar Basawa, Barden Ƙerarriyar Zazzau, Alhaji Haruna Abubakar, Bamalli shine uban taro a nasa jawabin hakimin yayi godiya ne da ƙoƙarin da Alhaji Lawal ya yi na zaburar da al'umma akan muhimmanci dasa itatuwa a rayuwar dan Adam.
Hakim ya ce dasa Itace na magance zaizayen ƙasa, dasa Itace na tace iskar da mutane ke shaka haka kuma kallon Itace na kara ƙafin Idanun Bil Adama
Ƙarshe Hakim ya nuna jin dadinsa sosai kuma ya yi fatan Alheri ga Alhaji Lawal bisa ƙokarin kawo cigaba da ya ke yi a garin Bomo.
Ya yi fatan samun cigaba da samun zaman lafiya a garin na Bomo da ƙasar Zazzau da jihar Kaduna da Najeriya baki ɗaya.
An yi taro lafiya an tashi lafiya.
No comments