Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan jihar Kebbi ya amince da cire kudi sama da naira miliyan dari takwas (814.8m) domin biyan kudin giratuti...
Daga Awwal Umar Kontagora
Gwamnan jihar Kebbi ya amince da cire kudi sama da naira miliyan dari takwas (814.8m) domin biyan kudin giratuti da hakkin ma'aikatan da suka rasu na ma'aikatan jihar su sama da dari hudu (417).
Gwamnan, Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya bayyana hakan ne domin amincewa da cire kudin don biyan kudin giratuti da ma'aikatan da suka rasu da ma'aikatan da suka aje aiki dubu dari hudu da goma sha bakwai (417) daga ma'aikatan gwamnatin Jihar da suka hada da kananan hukumomi, ma'aikatan hukumar ilimi na kananan hukumomi (LGEAs), da ma'aikatan da suka ajiye aiki da kashin kan su da suka aje aiki a tsakanin 16 ga watan Maris (16th March) da 15 ga watan Afrilu (15th April) na wannan shekarar ta 2024.
Wannan bayanin dai ya fito ne daga wata takarda mai dauke da sanya hannun sabuwar shugabar ma'aikatan Jihar mai rikon kwarya, Hajiya Aisha Usman wacce aka fitar kuma aka rabawa manema labarai garin Birnin Kebbi ranar asabar 5/10/2024.
Takardar ta yi karin bayani cewar mutane 314 ne kwamitin Kwadago ta tantance kuma ya mikawa gwamnati wanda kudinsu ya kama ₦757,716,817.54.
Baya ga wadannan kuma kwamitin ya sake tantance wasu mutum 287 a karkashin ofishin shugaban ma'aikatan Jihar wanda kudinsu ya kama ₦633,966,544.07.
Haka kuma takardar ta fitar da bayanin jadawalin ma'aikatan da za'a biya wadannan kudaɗlden kamar haka:
1. Waɗanda suka yi ritaya daga aiki har da wadanda ma'aikatan wucin gadi na ₦388,128,140.22
2. Ma'aikatan da suka yi ritaya na kananan hukumomi: ₦114,126,590.75. Mutane saba'in da daya (71).
3. Mutane 72 da suka yi ritaya daga ma'aikatar LGEA, ₦131,711,813.01 wanda ya bada jimillar Kudi ₦633,966,544.07 na mutane 287.
Haka kuma an amince da wasu karin kudi ₦180,813,976.66 ga wasu wadanda suka yi ritaya mutum 130 da ba'a gama tantance su ba daga cikin ma'aikatan shekarar (2017-2024) wadanda yanzu aka kammala tantance su wanda hakan ya kawo jimillar Kudin ₦814,780,520.73.
Shugabar ma'aikatan, Hajiya Aisha M. Usman tayi jinjina da godiya ta musamman ga gwamna bisa irin kulawar da yake baiwa ma'aikatan jihar wadanda ke aiki a halin yanzu da kuma wadanda suka yi ritaya.
Shugabar, ta bayar da tabbacin cewar za'a cigaba da baiwa kowani ma'aikacin da yayi ritaya hakkinsa a duk lokacin da aka kammala tantancesu domin gwamna a shirye yake yaci gaba da biyan kowa hakkin sa.
No comments