Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NUMW Da MAN Sun Nuna Takaicin Su Yadda Jami'an Yan Sanda Suka Aukawa Dilolin ‘Yan Kasuwar Zinare A Minna

Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar leburori masu hakar ma'adanin kasa (Nigeria Union Of Mine Workers) da kungiyar 'yan kasuwar ma...

Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar leburori masu hakar ma'adanin kasa (Nigeria Union Of Mine Workers) da kungiyar 'yan kasuwar ma'adanin kasa (Miners Association Of Nigeria) reshen jihar Neja sun nuna takaicin su kan wani samamen da jami'an yan sanda suka kai wa yan kasuwar ma'adanin kasa, inda suka kama mutane goma sha daya tare da kwace dukiyoyinsu.

Kungiyoyin sun nuna takaicin su ne a wani taron hadin guiwa da suka kira a sakatariyar NUMW ta jiha a safiyar Litinin din makon nan.

Tunda farko a bayaninsa, shugaban NUMW na jihar Neja, ya ce gwamnati ta kaddamar da kwamitin sanya ido wanda MARUFAWA Concept ke da alhakin tantance kamfanoni da 'ya'yan kungiyar don samar da kudaden haraji ga gwamnati, bayan sun bada goyon baya ga gwamnatin, "yanzu kuma jami'an 'yan sanda na Area Command da ke cikin garin Minna sun aukawa wasu dilolin mu tare da kwace dukiyoyin su da kayan aikin su", in ji su.

"Mun shirya wannan taron na hadin guiwa ne don neman mafita ga wannan kutsen na jami'an 'yan sanda suka yi, shin kudaden shiga na rijistar da gwamnatin jiha ta ce mu biya, ita ce a hakku ko jami'an 'yan sanda za mu biya kudin a hannun su. Domin ita dai kamfanin da aka dorawa alhakin kula da aikin muna ba ta goyon baya, amma kuma kamar jami'an yan sanda na zagon kasa.

"An kama mutane goma sha daya, mun biya kudin belin kowanne mutum daga dubu casa'in da hudu zuwa casa'in da shida kafin a sako su.

"Bayan nan kuma kayyayakin da 'yan sanda suka karbe a hannun su, su maido musu da kayan su; akwai wadanda an kwace kudaden hannun su bayan kudin beli, akwai wadanda zinaren da aka samu a shagunan su an kwace, wasu kuma na'urorin aikin su jami'an yan sanda suka kwace.

Kungiyoyin dai sun shawarci membobin su da su tabbatar duk wanda bai gabatar da kan shi ga wannan kwamitin ba, da ya tabbatar ya gabatar da kan shi tare da biyan harajin gwamnati ga MARUFAWA da kuma kiyaye ka'idodin da gwamnati ta gindaya, wanda duk ya cika ka'idodin ya samu wani barazana daga wata hukuma ko jami'an tsaro ya gaggauta sanar da uwar kungiyarsa ta jiha tare da bada bahasin irin cin zarafin da akai masa, "uwar kungiya a shirye take wajen bin hakki da kadin 'ya'yan kungiya, domin lauyoyin mu da na hukumar tattara bayanai da rijistan masu wannan harkar tsaye suke ba dare ba rana", in ji kungiyar.

Za mu sanya idanu akan abubuwan da ke faruwa ba, muddin mutum ko kamfani ko kungiyoyi sun bi ka'idodin gwamnatin tarayya da ta jiha akan harkar ma'adani. 


No comments