Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

‘Yancin Kan Nijeriya: Al’umma Su Dage Da Yi Wa Kasa Addu’ar Zaman Lafiya Da Samun Nasara, In ji Yanga

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar cikar Nijeriya shekaru 64 da samun yancin kai, ya kamata a rika tunawa da yan mazan jiya da suka ...


Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar cikar Nijeriya shekaru 64 da samun yancin kai, ya kamata a rika tunawa da yan mazan jiya da suka yi gwagwarmar ganin kasar ta fita daga kangin bauta, da kuma yi masu addu'o'in alheri kan rawar da suka taka wajen samun wannan yancin wajen hadin kai da ganin kasar ta tsayu da kafarta. Wani jigo a jam'iyyar APC da ya dade yana bada gudunmawa ga tsarin mulkin dimukuradiyya, Alhaji Hamza Yanga Buba ne yayi kiran lokacin da yake tsokaci kan cikar kasar nan shekaru 64 da samun yancin kai ga manema labarai a minna.

Alhaji Yanga, ya cigaba da cewar duk da muna ganin irin matsalolin da muke gani yau, wanda son kai da rashin kishin kasa ya janyo mana, da za mu yarda mu yi koyi da salon tafiyar magabatan mu da suka shude da matsalolin sun walwale a kankanin lokaci. Amma dukkanin wadannan matsalolin da muke gani yau tun daga kan shugabanni har talakawa kowa na da rawar takawa. Allah yayi muna gyadar dogo, tsoffin shugabannin mu irinsu Yakubu Gowon, Janar Babangida, Janar Obasanjo duk suna raye, ya kamata mu janyo su mu tattauna inda matsalar take a samo bakin zaren tare da yi masu addu'o'in alheri kan rawar da suka taka wajen dorewar kasar nan.

Dattijon kuma jigon siyasar, ya yabawa gwamnatin jihar Neja, bisa jagorancin babban manomi, gwamna Umar Mohammed Bago kan turbar da ya hawo na farfado da martabar jihar nan, na ganin tattalin arzikin noma da kiwo da ayyukan raya kasa da muka dade muna nema ya sanya su a gaba.

Wanda, muna da kwarin guiwar cewar yi masa addu'o'in samun nasara da goyon baya, Allah zai ba shi hikima da kwarin guiwar cigaba da ayyukan da ya sanya a gaba.

Yana da kyau, yan siyasa da masu kishin cigaban jihar nan, da su kawar da bambancin siyasa, jam'iyya dan goyawa gwamnatin nan baya, dan ganin samun wannan nasarar musamman kafa harsasan da zasu inganta tattalin arzikin jihar nan.

Yanga, yace kasar nan muna hanyoyin inganta tattalin arzikin mu, amma rashin kusantar masana da kwadayin tara abin duniya, yasa a kullun ake cikin korafi, yana da kyau mu dawo cikin hayacin mu, mu canja tunanin mu, mu zama masu kishin kasar da tabbatar da tsarin siyasa mai inganci sai mu samu mafita mai dorewa da za ta taimaka mana wajen ganin mun fita daga yanayin da muke ciki, amma hakan fa ba zai yiwu ba, dole sai mu kasance masu kishin kasa da son cigaban kasar da gaskiya, inji shi. 

No comments