Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mutanen Da Suka Yi Hasarar Dukiyoyinsu Sakamakon Rikicin Siyasa A 2003 Sun Nemi Tallafin Gwamnan Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Mutanen da rikicin zaben karamar hukumar Kontagora na 2003 ya shafa sun nemi tallafin gwamnan Neja, Hon. Umar Moha...



Daga Awwal Umar Kontagora

Mutanen da rikicin zaben karamar hukumar Kontagora na 2003 ya shafa sun nemi tallafin gwamnan Neja, Hon. Umar Mohammed Bago kasancewar halin da suka samu kan su na rashin madafa da kuma mummunar hasarar da su ka yi sakamakon rikicin.

Lamarin dai ya faru lokacin zaben kananan hukumomi da gwamnatin marigayi Injiniya Abdullahi Abdulkadir Kure ta shirya, inda aka gwabza tsakanin jam'iyyar PDP da PRP wanda jam'iyyar PRP ta lashe zaben, yayin da gwamnati mai ci a lokacin ta rantsar da dan takarar PDP, Hon. Sani Bello Mustapha (Basket) mai makon Haruna Buhari MK, inda hakan ya tunzura matasa suka aukawa manyan 'yan PDP a lokacin suka koma gidajen su da dukiyoyinsu.

Alhaji Muhammad Lawal Ibrahim (Hamdala) yana daga cikin wadanda suka yi hasarar dukiyoyi da muhallansu a lokacin. Ya ce tun faruwar lamarin har zuwa yanzu ba gwamnatin da tace mana uffan, saboda damuwa tasa wasu daga cikin sun mutu, wasun mu kuma muna fama da lalurorin rashin lafiya. Ya kara da cewa; "kamar ni da nake magana da ku yanzu haka ina fama da jinyar matsalar shanyewar jiki kuma da iyali ba yadda za mu yi. Bayan faruwar wancan iftila'in da ta same mu, da ni aka kafa jam'iyyar CPC da gwamna Umar Bago ya yi takarar dan majalisar tarayya kuma ya ci zabe, bayan dunkulewar jam'iyyun adawa inda aka samar da jam'iyyar APC da mu aka yi gwagwarmaya har aka kafa gwamnati tun daga gwamnatin Buhari zuwa wannan gwamnatin ta Tinubu da Bago, kuma har yanzu ba a ce mana komai ba", in ji shi.

"Muna kira da babban murya ga adalin gwamna mai nufin alheri ga talakawa da ya dubi girman Allah ya taimaka mana ko mun samu sassucin rayuwa. Muna cikin wani hali, da yawan mu ba sa iya rike gidajen su, ciyar da iyali na gagarar mu, ko da mukami na S. A ne mu samu ta yadda za mu rika samun abin sayen magani da ciyar da iyali", ya roka. 

No comments