Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Kebbi Ta Raba Kayan Abinci Ga Mutane Sama 27,000 Da Ambaliyar Ruwa Ya Shafa A Karamar Hukumar Mulkin Shanga

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya raba kayan abinci ga mutane 27,304 da matsalar ambaliya...



Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnan Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya raba kayan abinci ga mutane 27,304 da matsalar ambaliyar ruwa ta shafa a karamar hukumar mulkin Shanga.

Gwamnan wanda ya jagoranci raba wannan tallafin kayan abincin a garin Dugu da ke karamar hukumar mulkin Shanga.

A jawabin sa wajen kaddamar da rabon kayan abincin, gwamnan ya bayyana cewar wannan tallafin an bayar da shi ne domin rage wa al'ummar da ambaliyar ruwan ya shafa radadin wannan iftila'in da ya shafe su.

Ya yi kira ga al'ummar da su dauki wannan al'amarin da cewar wata jarabawa ce daga Allah.

Gwamnan ya kara da cewar in Allah ya yarda gwamnatin sa za tayi dukkanin abinda ya da ce wajen taimakawa al'ummar da ambaliyar ruwan ta shafa a jihar.

A bayaninsa, mai martaba sarkin Yawuri, Alhaji Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi CON FNSM, ya godewa gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu bisa wannan tallafin da ya baiwa al'ummar da ambaliyar ruwan ya shafa.

Sarki ya kara yi wa gwamna godiya ta musamman inda yace gwamnatin Kauran Gwandu tana kokari sosai ga al'ummar masarautar Yawuri domin babu wata matsala da za ta taso a wannan yankin gwamna bai shigo cikin lamarin ba kuma ya taimaka.

Sarkin Yawuri, ya yi addu'ar Allah ya kara yiwa gwamna jagora kuma ya cigaba da ba shi kariya da nasara da kwarin guiwa.

Shugaban karamar hukumar Shanga kuwa, Hon. Abdullahi Abdullahi Maiunguwaa jawabin maraba da ya gabatar a  taron ya nuna jin dadinsa bisa irin salon mulkin wannan gwamnatin ta jihar Kebbi karkashin jagorancin Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu.

Ya kara da cewar ayyukan maigirma gwamna, sun taba rayukan al'umma da dama wajen sanya su farin ciki a koda yaushe a kowani bangare na jihar Kebbi.

Hon. Bello Rilisco, shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Kebbi (SEMA), ya godewa gwamna bisa irin kokarin da ya ke yi wajen inganta rayuwar al'umma da taimakawa marasa galihu a fadin Jihar.

Ya cigaba da cewar sai yanzu jihar Kebbi ta samu gwamna mai kishin talakawa wanda a kullum burin sa ya inganta rayuwar talakawan jihar baki daya.

Daga cikin kayan abincin da aka raba sun hada da buhuhuwan shinkafa, gero da masara. 


No comments