Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Nuna Farin Cikinta Ga Hukumar NAPTIP Bisa Ceto Yara 'Yan Asalin Jihar

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan Jihar Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya nuna jin dadinsa bisa nasarar da hukumar NAPTIP ta...


Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnan Jihar Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya nuna jin dadinsa bisa nasarar da hukumar NAPTIP tayi wajen ceto yara  yan asalin Jihar su goma sha tara (19) daga hannun masu safarar mutane

Yaran akallan su goma sha tara (19)  yan asalin jihar Kebbi ne hukumar hana fatauci da safarar mutane ta NAPTIP ta ceto daga hannun masu safarar mutane a jihar Cross Rivers da ke kudancin kasar nan.

Tunda farko da yake jawabi a lokacin karbar yaran, Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu, ya bayyana godiya ta musamman ga hukumomin NAPTIP, gwamnati jiha, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), da hukumar NFIU da dai sauran hukumomin tsaro da suka bada gudunmawa wajen samun wannan babban nasarar.

Gwamnan, yace a yau na tsaya gaban ku cike da farin ciki a wannan lokaci da muke murnar samun nasarar ceto wadannan yaran daga hannun miyagun mutane masu safarar bil'adama. Ba zamu samu wannan nasarar ba idan bada hadin guiwar hukumar NAPTIP da sauran hukumomin tsaro ba.

Saboda haka a matsayin mu na gwamnati, za mu cigaba da iya kokarin mu wajen kare al'ummarmu da dukiyoyinsu musamman yara kanana masu tasowa daga fadawa hannun miyagun mutane domin yayan mu su yi rayuwa cikin yanayi mai cike da tsaro.

Wannan nasarar da muka samu wajen ceto wadannan yaran 19 daga hannun masu safarar mutane a birnin Calabar da ke jihar Cross Rivers a kudancin Nijeriya da sunan taimakon su wajen samun ilimi ya nuna irin kokarin da mu ke yi a gwamnatance wajen magance miyagun ayyuka musamman irin na safarar al'umma da saka su aikin bauta ".

Kauran Gwandu, ya kara da cewar gwamnatinsa za ta taimaka da dukkanin abinda ya dace wajen ganin yaran da aka ceto sun dawo cikin hayyacinsu bayan irin damuwar da suka shiga a lokacin da aka yi safarar su.

Daga karshe gwamnan yayi gargadi mai tsanani ga masu safarar mutane a jihar cewar tabbas gwamnati ba za ta sassautawa dukkanin masu gudanar da wannan mummunar sana'ar ba, cin zalin mutane musamman kananan yara.

Saboda haka gwamnan yace gwamnatin jihar Kebbi ba za ta lamunci wannan ba kuma za ta cigaba da baiwa hukumomi da jami'an tsaro hadin kai wajen kamawa tare da hukunta masu aikata irin wannan mummunan sana'ar.

A na shi jawabin, shugaban hukumar NAPTIP na jihar Kebbi, Alhaji Misbahu Kaura, wanda shi ne ya mika yaran da aka ceto ga gwamnan, ya bayyana cewar nasarar da suka samu a watan Yuli (July) da ya gabata ne wajen kama wani mutum daya daga cikin masu aikata wannan mummunan aikin ne ya ba su wannan damar wajen ceto wadannan yaran 19 daga jihar Cross Rivers.

Haka kuma ya bayyana cewar a lokacin da aka kama mutumin yana kokarin safarar wasu yara ne guda hudu (4) wanda hakan ya bada nasarar ceto sauran yaran 15 wadanda shekarun su ba su fi hudu (4) zuwa shida (6) ba.

Haka kuma ya bayyana cewar binciken su ya nuna mutumin ya fara wannan sana'ar safarar yaran ne tun cikin shekarar 2022 a jihar Kebbi.

Daga cikin yadda yake gudanar da aikinsa, mutumin yakan aje yaran ne a wani wuri a cikin garin Gusau na jihar Zamfara na kwana biyu ko uku a kokarin sa na ganin yaran sun saba da shi kamin daga baya ya wuce da su zuwa birnin Calabar.

Wasu daga cikin yaran da aka yi safarar tasu sun bayyana irin azabar da ake ba su a lokacin da aka yi safarar tasu wanda ya hada da sanya su ayyukan da su kafi karfinsu, duka da kuma saduwa dasu da dai sauransu. 

No comments