Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Kebbi Ta Kaddamar Da Kwamitin Shirya Bikin Kamun Kifi Na Argungu

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya kaddamar da kwamitin gudanarwar na shirya bukin k...



Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya kaddamar da kwamitin gudanarwar na shirya bukin kamun kifi na Argungu " International Fishing and Cultural Festival " da ake gudanarwa a kowace shekara a garin Argungu da ke masarautar Argungu a jihar Kebbi:l.

An kaddamar da kwamitin ne ranar a dakin taro na fadar gwamnatin Jihar wato "Government House's Council Chamber" da ke Birnin Kebbi.

Kwamitin da aka kaddamar ya kunshi mutun ashirin da daya karkashin jagorancin shugaban kwamitin mataimakin gwamnan jihar,i Alhaji Umar Abubakar Tafida da kuma sakataren kwamitin tsohon shugaban ma'aikatan jihar, sai kuma mai baiwa gwamna shawara akan harkokin hulda da ma'aikata, Alhaji Safiyanu Garba Bena.

A lokacin kaddamarwar, Sakataren gwamnatin, Alhaji Yakubu Bala Tafidan Yawuri ya bayyana sauran sunayen mambobin kwamitin.

Da yake jawabi a wurin taron, Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya bayyana gamsuwarsa da mambobin kwamitin inda yace yana da yakinin zasu gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata duba da irin shahararsu wajen ayyukansu da kuma tarihi mai kyau da suke da shi wajen nagarta.

Haka kuma, gwamnan yayi kira gare su da su yi bakin kokarinsu wajen ganin bikin kamun kifin da wasannin gargajiya yayi nasara kamar yadda aka samu nasara a bikin al'adun gargajiya na Rigata a masarautar Yawuri da kuma Uhola a masarautar Zuru.

Haka kuma, ya bayyana irin muhimmancin da bikin kamun kifin da wasannin al'adun gargajiyar na  "Argungu International Fishing and Cultural Festival " yake da shi wajen bunkasa al'adun gargajiya da kuma samar da kudaden shiga ga gwamnati.

Saboda haka ya nemi dukkanin mambobin kwamitin da su dage sosai wajen ganin bikin yayi nasara.

Ya kara da cewar abu ne mai muhimmanci ga gwamnatinsa ta ga cewar ta gudanar da wannan kasaitaccen bikin kafin ta cika shekaru biyu akan karagar mulkin jihar.

Ya nuna gamsuwarsa da kwamitin da aka zabo domin gudanar da wannan aiki karkashin jagorancin dan asalin masarautar kuma mataimakin gwamnan jiha saboda yasan ba zasu ji kunya ba da yardar Allah.

A wata mai kama da wannan kuma, gwamnan ya kaddamar da kwamitin rabon filaye wato "Land Use Act Allocation Committee" wanda Alhaji Kabiru Usman ya kasance shugaban kwamitin.

Gwamnan bayyana cewar dole za'a bi dukkanin ka'idodin da suka dace wajen raba filaye inda yace hakan zai kawo karshen kuraran da suke faruwa a wannan bangaren musamman kwacewa manoma filaye da ake yi ba bisa ka'ida ba. 


No comments