Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Halin Da Kasa Ke Ciki: Shawarwarina Ga Gwamnati, Masu Hannu Da Shuni Da Sauran Al'umma - Maryam Abacha

  Tattaunawar musamman da Jaridar MADOGARA ta yi da Hajiya (Dr) Maryam Sani Abacha Wannan ita ce tattauna ta musamman da tawagar jaridar Mad...

 

Tattaunawar musamman da Jaridar MADOGARA ta yi da Hajiya (Dr) Maryam Sani Abacha

Wannan ita ce tattauna ta musamman da tawagar jaridar Madogara ta yi da Hajiya (Dr) Maryam Sani Abacha, Uwargidan tsohon shugaban kasa, Marigayi Sani Abacha a gidanta dake birnin Tarayya Abuja. Tawagar jaridar ta tattauna da ita dangane da abubuwan da take ganin ya kamata a yi domin samun ci gaba da saukin rayuwa ga al’ummar Nijeriya. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance baki daya:

MADOGARA: An samu barkewar zanga-zanga a Nijeriya a kwanakin baya sakamakon matsin rayuwa da na tattalin arziki. A yayin zanga-zangar akwai garuruwa da musamman na jihohin arewa da aka yi hatsaniya da fashe-fashen kayan gwamnati da na al’umma. Mene ne ra’ayinku da shawararku akan wannan abu da ya faru?

Hajiya Maryam Abacha: Assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu. Mu iyaye ne. Dama ina so na yi magana ne a matsayina na ‘yar kasa, a matsayina na mace a matsayina kuma na Uwa. Kuma ina magana ne saboda ayyuka da muka yi da na gidan soja. Da kuma ayyuka da na yi na shugabar matan sojoji na Nijeriya gaba ki daya. Saboda Hafsan hafsoshi da kuma zama da na yi a Villa da irin ayyukan da na gabatar a lokacin da muke Villa na taimakon ‘yan Nijeriya da matasa da mata da yara.

Mun dai yi abubuwa, amma da yake ka san a kasar mu ana yin gwamnati wata gwamanti idan ta zo ba ta ci gaba da aikin da wata gwamnatin ta fara.  Sai a dakatar kuma sai su fara wani abu daban. To irin wannan ina jan hankali da ra’ayin al’umma da ‘yan siyasa kan cewa bai cika taimakon kasa da al’umma ba. Saboda ko ni kadai shirye-shiryen da na yi su ya kamata a ce da an ci gaba da su da sun taimaka. Da kuma wadansu abubuwan da ba su yiwu ba, da ba a yi su ba. Amma da yake an dakatar, to shiyasa aka samu abubuwa da suka faru.

Shi ne na ga ya cancanta na sake magana kuma a ja hankalin hukuma daga sama; shugaban kasa, da gwamna har zuwa kasa. Da kuma a ja hankalin masu kudi da abubuwan da ya kamata a yi kowanne Unguwa-Unguwa saboda a taimaki al’umma a kuma taimaki matasa. Domin yawancin zanga-zangar nan da aka yi, irin mu ba mu fita ba. Yara kuma kanana ba za su fito ba, duk irin ku masu karfi ne matasa suke fitowa. Kuma matasan nan yawancinsu ba su san tarihin irin abin da ya faru a kasa ba, ba su san abubuwan da ke faruwa ba. Kuma ka san yanzu an daina tarihi a kasa. To, bari na yi amfani da wannan lokacin na yi kira a kan cewa a dawo da karatun tarihi a kasa. Saboda idan matasa da yara ba su san irin tarihin abin da ya faru a kasa ba, ba za su san yadda za a ci gaba ba. Ya kamata su san tarihi, su san abin da aka yi masu kyau, su koya su yi. Ko kuma kurakurai da aka yi a yi gyara a kan su.

Kuma dama akwai shirye-shiryen da na yi a da a karkashin shirina na ‘Family Support’ (tallafawa iyali), to kuma da muka je Kano ma muka yi ‘Maryam Abacha Foundation’ na so mu yi. To amma kuma ni harkoki dai ta rayuwa ba su bar ni na yi su yadda nake so ba. Kuma ka da a ga kamar siyasa ce, wannan ba siyasa ba ce; damuwa ce bisa ga al’umma da kuma yara, tunda nima ina da yara da jikoki, kuma dukkansu matasa ne. To sai na zauna na rubuta wannan takarda; wannan takarda ita ce abubuwan da ya kamata a yi su.  Yanzu dama muna da kungiyoyin bijilanti akwai su a kasa; nake so a sake inganta su kowanne Unguwa.

Kwanan nan ma aka shiga gidan wata kawata nan Gwarinpa, Allah yasa ba su taba ta ba, suka dauke mata su mota su waya su talabijin harda akwatin kaya da sauran su. To ka ga dai duk dai ba dadi. To ka ga yaran nan ka ga da suna da abin yi, da ba za su mayar da kan su suna sace-sacen nan ba. Da mun yi wani shiri ana ce mishi ‘Family Economic and Advancement programme’ inda ake bayar da kudi, da kayan sana’a kuma a nemi sana’a da sauran su. To da a ce an ci gaba ka ga da yanzu mata ba za su yi talla ba, ba za su yi kamar shashanci ba, kuma za su yi zaman aure saboda suna da abin yi. Kuma ka ga matasa su ma za su samu abin hannu, su yi aure, su rike gidajensu. Ka ga ba za a yi irin wannan shashancin ba. Idan aka inganta kungiyar ‘yan bijilanti saboda a daina rikicin nan. Kuma su kansu idan suna wannan bijilanti din ka ga ba za su je su yi laifi ba. Idan suka yi laifi, ka ga za su kama kansu da kansu. Muke so kowacce Unguwa ba lallai Kano kadai ba, ko’ina a Nijeriya kowacce Unguwa a yi mata Islamiyyah, ko makarantar Coci; duk wanda suka ga ya fi cancanta; a kuma samo Malamai a koyar, ko Malaman Islamiyyah, ko Fastoci su koyar ma yara karatun addini yadda za su fahimta kuma a sanya musu Imani a zukatansu da hankulansu domin ka da su rika barna da yawa a gaba. Sannan kuma a horas da su yadda za su koyi sana’a (Vocational Training Centre), na bude ‘Vocational Training Centre’ da yawa a gidajen soja a da, kuma a nan Kano ni na bude Sani Abacha Youth Centre, a nan wajen hanyar Madobi. Amma ita ma yanzu ka ga kamar ita ma an kashe ta. Na bubbude makarantu a cikin bariki a Soja. Na bude makarantun koyon sana’a na mata. Na je na samu fili na bude makarantar koyon sana’a ga mata a cikin gari, idan aka yi a wata Unguwa, sai a fadada a yi a sauran Unguwa-Unguwa. To kuma su mutanen Kano din da kan su suka karkashe.  Ka ga ba a ci gaba ba ke nan, kuma ka ga irin wannan ba ni ake yi wa bakin ciki ba, wadanda za su koya su ake yi wa bakin ciki, ka ga ba a samu ci gaba ba.

Kuma ya kamata a samu kamar Bankin al’umma (Community Bank), a da an yi ‘Community Bank’, ya kamata a ce kowacce Unguwa a ce tana da dan ‘Community Bank’ saboda mutane su dunga kasuwanci, kuma ka da kai banki kudi da kawowa ya zama wani matsala ne saboda sata a hanya da kuma a bi ka har gida da sauran su. Idan a cikin Unguwar ne ka ga an san duk ‘yan Unguwar gaba daya.

Kuma ya kamata hukumar ‘yan sanda su bude kamar ofishin ‘yan sanda karami haka a kowanne Unguwa ya zama suna sanya ido akan yara. Abubuwan da ake yi da sauran su.

Kuma ya kamata a bude kamar gidan haihuwa na mata. Mu ka ga da muna da ‘Maternity Clinic’, to da akwai Unguwan zoma da yawa. Kuma akwai duba gari, suna duba tsaftar gidaje har rijiya, har ‘kitchen’ din mata har kwata da sauran su. Ya kamata duk wadannan a dawo da su a rika taimakawa. Kuma wannan shara da ake yi wata-wata da aka daina; yanzu duk kasa ta kamu da datti, kuma datti na kawo cuta, ta kamata a dawo da sharar kasarnan tunda bai rage ma mutum komai. Tunda bai wuce ka share kofar gidanka da Unguwarka ba. Tsaftace kai ai addini ne. Turawa ma sun ce ‘Cleanliness is next to godliness’, kuma tsafta ibada ne. Ya kamata a dawo da wannan tsaftar muhalli da Unguwa da sauran su.

Kuma ba mu da ruwa yawanci a Arewa; ya kamata kowanne Unguwa a yi musu ‘Borehole’ ko kuma a yi musu rijiya mai kyau a dunga samun ruwa. Ana sa famfo ‘yan Unguwar na samu suna dibar ruwa a ciki. A maimaikon kullum a siyar da ruwan nan da ba tsafta. Kuma ruwan nan ana yi kowanne Unguwa ka gani ko siyarwa za a yi a Unguwar ba zai yi tsada yadda za a dauka daga wani Unguwa saboda suna da ‘Borehole’ ba. Kuma gwamnati gaskiya tana da kudin da za ta taimaka a yi wadannan abubuwan.

To kuma wannan shi hukumar Almajiri (Almajiri Commision), ana yinsa a kasa. Ya kamata a ce kowanne gunduma a taimaka a yi musu suma da sauran su. Sannan kuma ya kamata a yi musu muhallin kamar bandaki. Mutanen mu sai su je a titi ana bawali ana bayan gida da sauran su. Wanda a addinance ma ba kyau. A kowanne hali ma ba kyau gaskiya, kuma ba ya kawo tsafta. Kuma wannan su bera da kuda za su je su tattaba, kuma ko mutum yana da cuta ka ga zai je ya taba wani abinci, kuma ana siyar da abinci a titi da yawa. Saboda kowanne wuri su yi na su ‘public toilet’ ko da ma biya za a yi da dan taro da kwabo ya fi a kan a rasa ba inda za a shiga. Wasu ana kulle ba za a shiga gidansu a shiga ‘toilet’ din su ba. Da gudun ma ka da a sa musu cuta. To ka ga ana da ‘public toilet’ zai yi taimako kwarai da gaske.

To kuma mu da muna yara akwai wani abu muna ce mishi kamar karamin kasuwa ne haka. To mu a Maiduguri ana ce mishi ‘Duriya’. To ‘Duriya’ din nan kamar karamar kasuwa ce haka. To kasuwar nan mutane ne maimaikon a je ana talla sai a kawo abinci a wurin ana siyarwa. To ka gani yanzu ana da kamar gidajen cin abinci haka nan. To amma da ana yin kamar ‘Duriya’ din nan ma ya yi. Masu Fura da Nono, masu gari masu gishiri masu maggi, kowa ya je ya siyar da hajarsa. Su Kuka, duk dai abubuwan da ake ci gaba daya. To kuma za ka ga kamar mutumin da yake siyar da nama ko kifi, zai je wurin zai ajiye kayansa. Duk dan Unguwar zai je ya siya. Wani dan Unguwar ma daban zai tsallaka ya je ya siya. To ka gani duk dai a cikin makwabta ne.

A da dai ana da gidan marayu ya kamata a ce a kowanne Unguwa, kowanne mai Unguwa yana yin abin da zai kula da maraya da marasa karfi. Domin marasa karfi suma kamar marayu ne. Ya zama marayan dole, to suma sai a rika taimaka musu. A samu kamar gidajen da suke kula da marayu da yara da gidajen kamar tsofaffi wadanda mazajensu suka mutu ba su da galihu sai suma a rika taimaka musu. Ko a ba su jari domin a taimaka musu. Ko a cikin Unguwar ne su dunga fita suna siyar da wani abu. A da muna gani muna yara tsofaffin suna yi, suna zuwa kasuwa suna siya suna siyarwa. Duk dai irin wadannan abubuwan suna yi, duk yanzu an daina su. Kuma yanzu gari ka ga duk babu tsaro. Ka ga idan ana yin irin wannan zai rika kawo tsaro haka nan.

Kamar irin wannan siyar da abinci, mai son sadaka sai ya kawo ya bayar ba sai ka je da kwarya ka ce, mu a Maiduguri sai a ce ‘Alaruya’, don Allah Mama a ba mu abinci, to muna yara ‘Alaruya’ ake yi, to mu ma a nan ana cewa ‘Allazi wahidun’. To ka gani irin wannan idan ana yin abincin nan, mai son bayar da sadaka sai ya yi abinci sai ya kawo sai ya ajiye. Na gani a talabijin akwai kasashen waje wadanda su ba ma musulmi ba kirista ba, amma masu kudinsu suna gina babban wuri gidan abinci; a sa tukwane, a sa kwanoni, a sa ruwa, a sa komai; duk mai wucewa mai jin yunwa ba sai lallai miskini ba, in dai kana wucewa kana son cin abinci, kuma abinci mai kyau, sai su zo sai a diban maka. Kwanon yana da sarka ba za ka iya tafiya da kwanon ba, kuma kofin mu na karfe ne, sannan suna da tsafta, suna wankewa suna gyarawa, ana sa magani sai su je su ci abinci. To mu ma masu kudin mu suna iya bude irin wannan gidan abinci. Kamar yanzu yadda ake yi a nan gidan Hajiya Mariya Sanusi; tana yin abincin sadaka shekara da shekaru, sai na ji bana ma kuma an je an kwashe kayan sadakan; ai ba zai hana su su ci gaba da sadakan ba tunda Allah ya hore. Amma ka ga ba dadi, tun wannan abinci dama domin al’umma ne. Don ka je ka dauka dama domin ku aka yi, amma ka gani ba ka dauka a hanyar daidai ba. Tunda ba ka tambaya ba kuma ba a baka ba, to ka gani duk dai bai yi daidai ba.

Sannan so nake a dunga zama ana addu’a ma kasa, kuma a yi ma jiha addu’a. Kuma a yi addu’a a kowanne Unguwa Allah ya shiryi yaranmu, Allah ya shiryi manyanmu, Allah ya shiryi komai da komai. Kuma duk abin da muke da shi Allah yasa ya yi kyau. Kuma ya kamata gwamnati ta dunga magana, kamar suna da hukumomi da yawa, a dunga magana a rediyo ana jawo hankalin mutane. Ba zancen siyasa kadai ba da zage-zage da barna da sauran su kadai za a dunga yi ba, a’a wannan ma ni ban ce a daina ba, amma idan aka daina din, ya fi alheri. Gwara a dunga fadakar da mutane a kan abubuwan alheri da mutane za su rika yi. Ko a kira Malamai, ko masu ilimi a zo a rinka yin abubuwan taimako da sauran su.

To irin wadannan abubuwan da duk na fada, da kuma wani abu da duk wanda yake da abin da ya fi wannan, ko kuma yake kama da wannan. Da kuma wanda yake da abin da zai fada na taimakawa duk sai a fada. Domin kasa ta mu ce, al’umma ta mu ce, kuma duniyar nan kwana nawa muke. Jiya-jiya aka haifoka, gobe-gobe ka tafi. To ka ga a tsakankani da muke zaune a ciki sai mu taimakawa junanmu, mu taimaka ma ‘ya’yanmu da jikokinmu, da al’umma gaba daya saboda a samu zaman dadi.

Za ka ga kasashe wadanda ba ma addini suke, amma suna da tsari a rayuwa. Tsarinsu yana tafiya daidai komai, yana yin daidai kuma ba mishkila. To ka ga mu ma me yasa ba za mu koyi irin wannan ba? A dunga koya ma yara sana’a, a koya musu da’a a koya musu abubuwa, amma an bar yaranmu karazube. Sai kuma mutum ya je ya auro mata, ni fa musulma ce ban ce ka da a yi aure-aure ba, amma sai ka je ka auri mata; kaima lebura ne, matarka tana leburanci, to ‘ya’yan nan sai a ce an kai su karatun Allo, to ka ga kowanne Unguwa idan suna karatun Allo, to ka ga ‘ya’yanka ba za su yi nisa ba. Abin nan ba lallai sai a cikin gari ba, ko a kauyuka da kuma Unguwa-Unguwa, sai a je a yi. Ka ga ba za ka kai danka wani gari ya je ya lalace ba, ya galabaita ya zama ba kula ba.

MADOGARA: Idan na fahimci Inna, wannan abin ba ya takaita ga gwamnati kadai bane, da masu hannu da shuni da talakawa da kowa da kowa su hadu domin su aiwatar da wannan abu?

Hajiya Maryam Abacha: Shi ne na ce da masu hannu da shuni, da wanda suke da gwamnati a matakin tarayya da jiha da kananan hukumomi. Ba a ce mutum daya ya dauki wannan nauyi ba. Amma kowa, an ce ba da hannu daya ake dora jinka ba. To ai ka ga ko Nijeriya ana yin hoton ta da hannaye da yawa sun da ga Nijeriya. To ai ka gani kowanne Unguwa, kowanne al’umma da ga kan mu za mu yi. Ya kamata kowanne al’umma mu da ga kan mu, mu taimaki kan mu mu taimaki juna, abubuwa su tafi yadda za mu ji dadin rayuwarmu. Amma mune duk wani kwata an cika da leda. Gaskiya zaman mu ba da’a, ya kamata gwamnati ta duba daga matakin tarayya zuwa jiha a duba a gani a mayar da da’ar nan, duk fa muna da da’a. Kawai ganganci ne da rashin sakawa. Amma idan mutum ya sa kan shi, aka saka shi ya yi, za a yi. Su kasashen nan, mun je kasashe da yawa gaskiya suna da da’a. Kuma za ka ga kasashen su akwai tsafta. Akwai abubuwan da aka jejjera ana bi. Ko a kasar waje, ko a nan ba na yi, ko ina mura idan na cire majina sai na sa a cikin aljihu ko a cikin jakar hannu na, idan na zo gida sai na saka a shadda ko ‘dustbin’. To amma ka ga bai kamata kana tafiya ka rika tofar da miyo ko majina ba a titi ba. Ka ga ka baza cuta, tunda mura ma ai cuta ce. Ko kuma ka je ka tsaya ka yi bawali, ko ka yi bandaki; duka wadannan abubuwa ya kamata a ce Nijeriya yanzu ta girma; an daina haka. Mu din nan mu muka yi faretin samun ‘yancin kai harda ‘self-government’. To ka ga yanzu ai ya kamata a ce mu Nijeriyar kanta ta girma ta kai shekarun mu, ka gane ko? Ya kamata a ce muna da da’a; balle mu arewar mu gaskiya. Arewarmu ya kamata; shugabannin mu da manyanmu su tashi sosai.

Kuma ina da jan kunnen jama’a kan cewa; ana fada, Malami su fito, ‘yan siyasa su fito, ‘yan adawa, kamar adawa a siyasa, muna zargin juna; ai ba a yi kaza ba. To, idan ba ka yi wa kanka ba, babu mai yi maka. Yanzu irin wannan da a ce an taru an dade ana yi, kamar yanzu PTF, ka ga ni na fara PTF a Nijeriya, sai gwamnati ta dauka ta dunga yi. Ka ga da a ce an ci gaba da PTF; da an kula da makarantu, an kula da asibitoci, an kula da tituna, an kula da al’umma. To duk abin nan sai aka zo aka kashe saboda wane ne ya yi, ba ma son shi, ba ma son gwamnatin shi. Shi kuma ya yi wa al’umma ne. Duk wannan abin ba shi aka yi wa ba. Kamar shi Maigida ai ba ma ya duniya, to ai ka ga ba shi aka yi wa ba, bai sani ba ma an daina yin wadannan abubuwan. To ka ga bai dame shi ba. To, amma mutanen nan da aka hana su wannan ci gaba, su zai dama. Sune ka ga ba su ji dadi ba. An hana su rayuwa mai inganci.

MADOGARA: A karshe wani kira kike yi ga shugabanni da talakawa da masu hannu da shuni domin ganin an aiwatar da wadannan abubuwa da kuka bada shawarar a yi?

Hajiya Maryam Abacha: Shi ne nake cewa su manyan su ji tsoron Allah su yi ma na kasa da su adalci, wanda ana kokartawa daidai gwargwado, su kuma na kasan ya kamata su dunga nuna godiya da tawakkali. Kuma su dunga nuna kan cewa; abin da ake yi mana mungode. Allah ya ce idan ka gode min, zan kara maka. Balle mutum. Kakaki yau ka min abin alheri, nagode, ka ga gobe sai ka kara kyautata min. Amma idan ba a yi haka ba, ka ga ba kyautatawa. To kullum idan ka tashi kana zagin kasa, kana zagin gwamnati, kana zagin gwamna, kana zagin minista. To mu ‘yan adam ne, kuma dan Adam ajizi ne, ba cikakke bane ba.

To ya kamata gaskiya a ji tsoron Allah a bi Allah. Kuma ya kamata su na kasan su nemi abin yi kamar yadda na fadan nan, idan aka taimaka musu su karba su yi. Ba za ka zama babban mutum a rana daya ba, ba za ka zama miloniya a rana daya ba. Ko da Babanka mai kudi ne, kaima sai ka dora. Idan ba haka ba, za ka zauna ka ci wanda ya hada maka ne, kuma zai kare. Rayuwar haka take, kowa ya koyi nema. Kuma ya koyi gyara abin da ya nema din. Kuma ya koyi kyautatawa, to idan muna kyautatawa junanmu, muna nema; kowa zai samu abin yi. Mutum ba zai samu lokacin irin wannan barna ba. Kalli matasan nan na ji tausayinsu, su fita suna ihu; ba ilimin, ba kudin, ba wannan, ba wancan, abin ba dadi. Sun fita kuma sun je kamar da bakin ciki da neman kamar sakayya; wannan ba sakayya ba ce. Ka je ka fasa rumbun mai kudi, ka kwashe mishi. Shi fa da guminsa ya nemi kudin nan, kuma ka ga ka yi laifi, Allah zai kama ka. Ka je gidan gwamnati kai da kake so a gyara, ka je ka bata. To ai idan kana neman gwamnati ta gyara, ka je ka bata mata. To matar da take so aurenta ya gyaru sai ta zuba ma mijinta borkono ko gishiri da yawa a abinci. To ai ka ga ba zai ji dadi ba, kuma ba zai kyautata mata ba. Amma ka gani matar na tuba an ce ba ta rasa miji, mu mu zama muna da kirki gaskiya. Kirki yana da amfani, mu zama mutanen kirki mu zama masu da’a masu ladabi, masu biyayya, masu kuma kula da kan mu da junanmu. Kuma akwai makwabtaka, a kiristanci ma, a musulunce ma, a ko’ina, ya kamata ka kula da na kusa da kai da makwabcinka, da wanda suke aiki a karkashinka da wanda kuke aiki tare da sauran su dai. Ya kamata mu kula da junan mu, Allah ya taimake mu kawai.

MADOGARA: Mungode.

Hajiya Maryam Abacha: Alhamdulillah!

 

No comments