Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar leburori masu hakar ma'adani a jihar Neja ta yi karin haske dangane da batun rijistan masu hakar ma...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kungiyar leburori masu hakar ma'adani a jihar Neja ta yi karin haske dangane da batun rijistan masu hakar ma'adani a jihar Neja. Shugaban kungiyar ta kasa reshen jihar Neja, Kwamared Musa Adamu Nasko ne ya yi wa manema labarai karin hasken yammacin Juma'ar nan a Sakatariyar kungiyar da ke Minna.
A cewar Shugaban a harkar kasuwancin ma'adani ya kasu amma gwamnati na magana ne akan manyan kasuwa da ke zaune a shagunan su cikin kasuwa, da kananan yan kasuwa da ke shiga daji suna sayo ma'adani da wadanda ke zaman kan su a kawo su siya su sayar wadanda ake cewa 'vendors', kowa da farashin da aka kayyade masa na rajista.
"Su kuma kamfanoni suna nan suna zama da gwamnati domin samun daidaito, wanda kuma tattaunawarsu da gwamnati ta yi nisa. Maganar leburori da karkashin kungiya kuwa, yanzu haka muna tattaunawa ta yadda gwamnati za ta rika samun kudin shiga a hannun mu, wanda idan mun kammala za mu sanar kuma muna da kudurin shirya babban taron da za mu kira dukkanin kananan hukumomi domin su san matsayin kungiya da kuma yarjejeniyar da muka cin ma da gwamnati", in ji shi.
Ya ci gaba da cewa; "Saboda muna kara kiran 'ya'yan kungiyar mu da babban murya duk wanda bai rijista da kungiya ba, ya tabbatar ya gaggauta yin rajista don mallakar katin zama dan kungiya, wanda duk wata barazanar da lebura zai fuskanta muddin bai da rijista wanda shi zai sa ya samu katin shaidar zama dan kungiya, ba ruwan mu da shi.
"Kuma kungiya za ta ci gaba da hadin kai da gwamnati dan tantance na kwarai da bata gari, saboda rika shebur ko shiga rami wajen neman ma'adani ba shi zai sanya ka zama dan kungiya ba, dole sai ka bi ka'idodin kungiya.
"Kungiyar mu kungiya ce wadda gwamnatin tarayya taiwa rajista kuma ta hada da kungiyar kwadago ta kasa ( NLC), dan haka a matsayin mu na yan jiha masu son cigaba za mu cigaba da hada kai da gwamnati wajen tsalkake sana'ar mu", ya karkare.
No comments