Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Adamu Shika Ya Bai Wa Matasa Shawara Akan Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kaduna

Daga A'isha Suleiman Zariya Dan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar Giwa ta Gabas kuma mataimakin shugaban masu rinjaye a majali...



Daga A'isha Suleiman Zariya

Dan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar Giwa ta Gabas kuma mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar  jihar Kaduna Honorabul Adamu Muhammad,Shika yayi kira ga matasan karamar hukumar Giwa da jihar Kaduna baki É—aya akan zaÉ“en kananan hukumomi mai zuwa nan da kwana 7 masu zuwa da cewa su bayar da goyon baya ayi zaben cikin kwanciyar hankali tare da kaucewa duk wani fitina ayi shi lafiya shine ci gabanmu baki É—aya.

Honorabul Muhammad Shika yayi wannan rokonne yayi da yake zantawa da manema labarai jim Æ™adan bayan ya kammala gabatar da jawabi a wajan taron bukin  yaye É—alubai na Shehu Usman Fashion Academy da ya halatta a bubban É—akilin taro na Tanimu Balarabe dake harabar IAR jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Honorabul Adamu Muhammad,Shika ya kada baki yace shi zabe al'amarine na Allah mai kowa mai komi domin shi Allah ya riga yasan wanda zai ci zaben mu namu jirane kawai a matsayinmu na 'yan Adam.

Bisa haka ne ÆŠan majalisar yayi roÆ™o ga dukkan al'ummar Æ™aramar hukumar Giwa da jihar Kaduna baki É—aya dasu taimaka wajan gudanar da wannan zaben lafiya domin hakan zai  Æ™arawa zaman lafiyarmu inganci.

Da Ɗan majalisar yake amsa tambayoyi manema labarai akan ƙalubalen da ƙaramar hukumar tasa take fuskanta a halin yanzu sai yace, " A gaskiya mun godewa Allah domin ana samun taimakon Allah a cikin lamarin sosai"

Dan majalisar dokokin ya kara da cewa, ba ƙaramar hukumar sa ƙadai ke fama da matsalar tsaronba yace amma duk da hakan suna godiya ga Allah kuma muna jinjina ga Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani bisa namijin ƙokarin da yake yi a kan batun tsaro.

Bisa haka ne Ɗan majalisar yace, yana kira ga dukkan al'ummar ƙaramar hukumar ta Giwa da suyi hakuri su ci gaba da addu'a saman zaman lafiya mai ɗorawa.

Ƙarshe yayiwa taƙwaransa Honorabul Abubakar Jamil Albani fatan alheri bisa tsayawarsa takaran kujerar shugabancin ƙaramar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna a wannan zaɓe mai tahowa.

No comments