Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mutum 94 Sun Kone Kurmus, 50 Sun Samu Munanan Raunuka Bayan Faduwar Tankar Mai A Jihar Jigawa

Daga Abubakar M Taheer A ranar Talata da misalin sha daya na dare wata Tanka dauke da Man futur data taso daga Kano zuwa Nguru ta fadi a kus...


Daga Abubakar M Taheer

A ranar Talata da misalin sha daya na dare wata Tanka dauke da Man futur data taso daga Kano zuwa Nguru ta fadi a kusa da Khajida University  Majia.

Cikin wata sanarwar Gaggawa da jami'an hulda da jama'a na hukumar yan sanda ta Jihar Jigawa DSP Shiisu Lawan Adam ya fitar da safiyar yau, ya bayyana yadda lamarin ya afku.

Bayan faduwar Tankar keda wuya man ya rinka kwarara magudan ruwa Wanda Al'ummar garin suka fito domin kwasar man Fetur din, anan take wuta ta kama inda nan take Mutum 94 sun kone kurmus. Sauran Mutum  50 kuma sun samu munanan raunuka inda aka garzaya dasu babban asibitin Ringim domin karban Magani.

Kwamishinan Yan Sanda CP AT Abdullahi  ya jajantawa Al'ummar Majia dama jihar Jigawa baki daya kan wannan iftila da samesu tare da adduar Allah ya jikan Wanda suka ragamu gidan gaskiya.

Ya kuma bukaci Al'umma da su rinka kulawa sosai da lamarin faduwar tankar Mai Wanda take saurin kamawa da wuta bayan faduwar ta.

Zuwa hada wannan rohoton al'ummar garin na Majia na cikin halin kaÉ—uwa bisa wannan mummunan ifitila'i daya afka musu.

No comments