Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Tsinci Gawarwaki Sha Biyu Da Ake Tunani Na Ƴan Bindiga Ne A Abuja

  Ƙauyan Tokulo da ke ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun shiga ruɗu sakamakon tsintar gawarwaki guda da aka yi a garin ...

 


Ƙauyan Tokulo da ke ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun shiga ruɗu sakamakon tsintar gawarwaki guda da aka yi a garin da ake tunanin ƴanbindiga ne.

Kansilan mazaɓar Igu a yankin, Jerry Alkali ya shaida wa Daily Trust cewa mutane ne suka kira shi da misalin ƙarfe 2 zuwa 3 na daren Litinin, cewa suna ta jin harbe-harbe.

Ya ce, "ranar babu wanda ya iya barci. Da safiya da mutane suka fara zuwa tafiya zuwa gona suka fara ganin gawarwaki a wata hanyar tafiya ƙaramar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna," in ji shi.

Jaridar mai zaman kanta ta ruwaito cewa mutanen garin sun ce a cikin gawarwakin babu ɗan garin, wanda a cewarsu ke nufin ko dai an kashe a musayar wuta, ko kuma an kashe ne a wani wurin daban, aka kwaso gawarwakin aka kawo ƙauyensu.

Har zuwa lokacin haɗa labarin a a samu kakakin rundunar ƴansanda Abuja Josephine Adeh a waya ba.

No comments