Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojoji Sun Ce Sun Kashe Ƴan Bindigar Da Suka Je Karɓar Kuɗin Fansa A Kaduna

  Sojoji sun kashe wasu da ake zargi ƴanbindiga ne a daidai lokacin da suke niyyar karɓar kuɗin fansa a ƙauyen Mai-Iddo da ke ƙaramar hukuma...

 


Sojoji sun kashe wasu da ake zargi ƴanbindiga ne a daidai lokacin da suke niyyar karɓar kuɗin fansa a ƙauyen Mai-Iddo da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sojojin bayan kashe ƴanbindigar, sun koma ceto mutanen, waɗanda uku mata ne, da wani yaro ɗaya da aka sace a makon jiya.

"An yi tsari ne da sojojin a kan cewa wani mutum zai je kai kuɗin fansa, su kuma su bi baya. Haka kuwa aka yi, ƴanbindigar na fitowa sai sojojin suka fito, suke buɗe musu wuta, suka kashe su a nan take," kamar yadda wani jagoran al'umma ya bayyana wa Daily Trust.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, kakakin ƴansandan Kaduna bai yi magana kan lamarin ba.

No comments