Daga Abubakar Musa, Zariya A yau Asabar 19/10/24 hukumar zaɓe ta jihar Kaduna ta ayyana a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓukan kujeru...
Daga Abubakar Musa, Zariya
A yau Asabar 19/10/24 hukumar zaɓe ta jihar Kaduna ta ayyana a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓukan kujerun kansiloli da na shugabannin ƙananan hukumomi a duk fadin jihar ta Kaduna.
Wakilinmu ya halarci ƙaramar hukumar Sabon Gari domin ganewa idonsa halin da ake ciki. Honorabul Abubakar Jamil Albani wanda shi ne ɗan majalisar jihar mai wakiltar gundumar Basawa ta ƙaramar hukumar Sabon Gari kuma shi ne ɗan takarar kujerar ƙaramar hukumar ta Sabon Gari a wannan lokaci.
A yayin kammala jefa kuri'arsa a akwatinsa da ke a makarantar Sa'eedu Primary School mai lamba (012 Samaru) ya zanta da manema labarai kuma ya ce, "Da ikon Allah jam'iyyar APC ce za ta sami nasara cikin yardar Allah."
Kuma ya shawarci dukkan al'umma da su zama masu bin doka da oda a kowani lokaci a kuma a kowanne yanayi.
Tuni jama'ar da ke wannan mazaɓa suka nuna goyan bayansu ga dan takarar tare da take masa baya zuwa gidansa.
An ci gaba da jefa kuri'a ba tare da samun wani tsaiko ba.
Yanzu haka mutanen karamar hukumar ta Sabon Gari sun natsu don jin sakamakon zaben.
No comments