Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya amince da dakatar da kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musamman kuma memba a majalisar zartarw...
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya amince da dakatar da kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musamman kuma memba a majalisar zartarwa ta jihar, Auwalu Danladi Sankara nan take, har sai an gudanar da bincike kan zargin da hukumar Hisbah ta jihar Kano take yi masa.
Sanarwar dakatarwar ta
fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren gwamnatin jihar Jigawa
Malam Bala Ibrahim.
Rahotanni daga jaridar Daily
Struggle na cewa, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano a ranar Juma’a ta tabbatar da
kama Auwalu Danladi Sankara, wanda ake zargin an same shi da wata matar aure a
wani gini da ba a kamala ginawa ba.
Darakta Janar na
hukumar, Dakta Abba Sufi, ya tabbatar wa manema labarai kamun. Ya ce an kama
shi ne ta hanyar bin diddigi bayan samun wasu korafe-korafe daga kanin mijin
matar auren da Kwamishinan yake bibiya.
“Eh gaskiya ne, mun kama Auwal Danladi Sankara, Kwamishinan Jigawa tare da wata matar aure a wani gini da ba a kammala ba.
“Bai san cewa muna bibiyarsa ba bisa rahotannin da muka samu a kansa,” in ji Dakta Sufi.
A cewarsa, kama shi ya
biyo bayan korafin da Nasiru Bulama, mijin matar ya yi, inda ya zargi
kwamishinan da yin lalata da matarsa, Tasleem Baba Nabegu, mahaifiyar ‘ya’yansa
biyu.
“Nasiru Bulama ya
shigar da karar ne ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano, da ma’aikatar tsaro ta
DSS, da kuma hukumar Hisbah, bisa zargin Sankara da hannu wajen lalata da
matarsa,” in ji jami’in.
Shugaban hukumar ya
bayyana cewa za su gurfanar da Sankara a gaban Kotu a kan wasu kararraki da ake
yi masa da suka hada da gudanar da ayyukan haramtattun kwayoyi masu suna
Picklock, 360 da sauransu.
Kazalika sanarwar da
jami’in hulda da jama’a na ofishin Sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Ismail
Ibrahim Dutse ya fitar a ranar Asabar, ta ce matakin ya zo ne bisa la’akari da
ikirari na baya-bayan nan da yake bukatar bincike domin tabbatar da gaskiya da
kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana na Gwamnatin Jiha.
Sakataren gwamnatin ya
jaddada kudirin Gwamna Malam Umar A. Namadi na tabbatar da gaskiya da kuma bin
ka’idojin da’a wajen gudanar da mulki.
“Dakatarwa da aka yi masa
wani mataki ne na riga-kafi da aka yi domin ganin an gudanar da bincike na
gaskiya,” in ji Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim.
“Muna daukar duk
zarge-zargen da muhimmanci kuma mun himmatu wajen tabbatar da amanar 'yan
Jigawa a gwamnati.”
No comments