Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ranar Abinci Ta Duniya 2024: Manoma Mata Sun Yi Bikin Baje Kolin Abin Da Suke Nomawa A Zamfara

Daga Hussaini Yero  Kungiyar Mata Manoma wato 'Nigerian Association of Women in Agriculture' reshen jihar Zamfara tare da Hadin guiw...




Daga Hussaini Yero 

Kungiyar Mata Manoma wato 'Nigerian Association of Women in Agriculture' reshen jihar Zamfara tare da Hadin guiwar Ofishin matar Gwamnan jihar Hajiya Huriyya Dauda, sun gudanar da bikin ranar abinci ta duniya inda suka baje kolin hajar su na amfani gona da kowacce karamar hukuma ke nomawa, a gidan wasannin yara da ke Gusau babban birnin jihar.

A jawabin ta Uwargidan gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Hajiya Huriyya ta bayyana cewa, wannan rana, rana ce da Majalisar dikin duniya ta ayyana a matsayin ranar abinci ta duniya, "muma matan jihar Zamfara, ba a bar mu a baya ba wajen nuna ma duniya amfanin gona da muke nomawa domin dogaro da kai da ci gaban tattalin arzikin jihar mu da kasar mu baki daya".

"Kuma a yau gamu mata manoma mun fito daga cikin kananan Hukumomi da kalolin abincin da  mu ke nomawa da kuma yadda mu ke sarafa shi ya zuwa abinci. A don haka insha Allah a shekara mai zuwa mata manoman jihar Zamfara za su bada mamaki wajen kara kaimi na zuwa da amfanin gona da mu ke nomawa da hannun mu", in ji Huriyya Dauda.

Huriyya Dauda ta jinjin ma kugiyar karkashin jagorancin Shemau Nalado akan zamowarta kallabi tsakanin  rawuna a ci gaban noma.

Babban bako mai jawabi Kwamishinan Kananan Hukumomi da masarautu na jihar Zamfara, Hon. Ahmad Yandi ya bayyana cewa, kudirin wannan gwamnatin jihar Zamfara shi ne bunkasa noma. Wanda ya ce wanann shi ne dalilin da ya sanya gwamna Dauda Lawal ya raba takin zamani da ingantacen iri kyauta ga manoma jihar domin samun ingantacen abinci da bunkasa tattalin arzikin jihar. 

A nata jawabin shgaban kungiyar, Shemau Nalado ta bayyana cewa, sun baje kolin abin da suke nomawa ne ga duniya domin a ga zahiri da kuma ci gaban da membobin kungiyar suka samar na amfani gona da ake nomawa.


No comments