Daga Hussaini Yero Ofishin Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta yi hadin guiwa da AGILE a wani shiri na musamman domin ...
Daga Hussaini Yero
Ofishin Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta yi hadin guiwa da AGILE a wani shiri na musamman domin unkasa ilimi 'ya'ya mata a fadin jihar domin ceto rayuwar su daga halin da suke cikin na rashin zuwa makaranta.
A jawabin matar Gwamnan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa, a cikin wannan watan ne majalisar dinkin duniya ta ayyana ranar 11 ga Oktoba a matsayin ranar yara mata ta duniya domin amincinsu da 'yancin 'ya'ya mata da magance kalubale zuwan su makaranta.
"Gwamnatinmu ta sanya ilimi a kan gaba a cikin kudirin ta guda shida, tare da mai da hankali sosai wajen ganin an bai wa ‘ya’ya mata ilimi mai inganci a matsayin hanyar da za ta kai ga samun haske a gobe. Mun yi imanin cewa idan 'yan matanmu za su yi nasara a duniyar yau, dole ne su sami ingantaccen ilimi, musamman a fannoni kamar Kimiyya, Fasaha, Injiniya, da Lissafi wanda ke cikin shirin (STEM).
"Kuma wannan shirin wani yunÆ™uri ne na haÉ—in gwiwa tsakanin ofishina da AGILE. Shiri ne da taimakon Bankin Duniya da Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya. Makasudin wannan shirin shi ne don inganta ilimin sakandare da samar da dakin gwaje-gwajen a Makarantun Sakandare na ’yan mata da kayan aikin gwaje-gwaje na zamani a matsayin wani É“angare na Æ™oÆ™arinmu na haÉ“aka karatun STEM", in ji ta.
Ta karkare da cewa; "a karshe ina jaddada aniyar gwamnatin mai girma Gwamna Dauda Lawal na tallafawa shirin ilimantarwa ‘ya'ya mata a karkashin shirin AGILE da kuma kudinrinsa na bunkasa ilimin ‘ya’ya mata da karfafa musu gwiwa. Za mu ci gaba da Æ™arfafa waÉ—annan tsare-tsare tare da tabbatar da cewa kowacce yarinya a jiharmu ta sami damar yin karatu da kammala shi."
No comments