Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Kebbi Ta Kaddamar Da Fara Aikin Wasu Tagwayen Hanyoyi A Argungu

  Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnatin jihar Kebbi ta kaddamar da aikin tagwayen hanya mai tsawon sama da kilomita shida (6.4km) a shiyar tso...

 

Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnatin jihar Kebbi ta kaddamar da aikin tagwayen hanya mai tsawon sama da kilomita shida (6.4km) a shiyar tsohuwar Bypass da ke garin Argungu.

Gwamnan jihar, Kwamared Nasiru Kauran Gwandu ya kaddamar da aikin a garin Argungu in da mai martaba Sarkin Argungu Alhaji Dakta Sama'ila Muhammad Mera ya samu halarta.

Da yake jawabi a wurin taron kaddamar da aikin, Gwamna, Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya bayyana cewar wannan yana daya daga cikin alkawarin da suka dauka a lokacin yakin neman zabe da kuma kokari da gwamnatin sa take yi wajen raya kauyuka da birane a fadin jihar.

Haka kuma ya bayyana cewar aikin hanyar ya hada da gina hanyoyin ruwa/kwalbatoci da kuma sanya fitilun titi mai aiki da hasken rana wato " solar powered street lights ".

Gwamnan, ya bayar da tabbacin cewar  gwamnatinsa  za ta sanya ido sosai wajen tabbatar da an yi aiki mai inganci.

Gwamnan ya kara da cewar tuni ya amince da biyan kaso arba'in na aikin saboda haka ba za'a samu matsala ko tsaiko a aikin ba saboda matsalar kudi ba.

Gwamnan ya cigaba da cewar nan bada jimawa da za'a kara kaddamar wasu ayyukan a wurare daban-daban a karamar hukumar ta Argungu inda yace zasu tabbatar itama masarautar Argungu an samar da ingantattun ayyukan cigaban al'umma dan daga martabar masarautar a jihar Kebbi.

Gwamnan yace wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu ciki har da bangaren ilimi tare da yin godiya ta musamman ga mai martaba sarki bisa goyon baya da gudummawar da masarautar Argungu take bashi.

Da yake jawabi a taron, gwamna Nasiru Kauran Gwandu ya bayyana cewar sati mai zuwa za'a kaddamar da fara aikin gyaran babban asibitin gwamnatin Jiha da ke Argungu.

A nasa jawabi a wurin taron, Kwamishinan ayyuka Hon. Injiniya Abdullahi Umar Faruk yayi godiya ga Allah da ya nuna musu wannan ranar ta kaddamar da fara aikin inda kuma yayi yabo da jinjina ga Gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu bisa irin ayyukan cigaban al'umma da yake gudanarwa a fadin Jihar baki daya.

Haka kuma ya yabawa gwamnan bisa cika alkawarin da yayi a lokacin yakin neman zabe da kuma gudanar da wasu sabbin ayyukan daban.

Kwamishinan ya bayyana yadda zai kasance inda yace aikin ya shafi gina sama da kilomita shida (6.4km) mai tagwayen titi wato Dual carriageway, gina kwalbatoci a gefen hanyar saboda inganta aikin hanyar, sanya fitilun titi masu aiki da hasken rana da dai sauransu.

Ya bayyana cewar kamfanin Amirco Universal Concept Ltd ne zai yi aikin kwangilar aikin hanyar akan kudi sama da biliyan bakwai (₦7.23b) a cikin watanni goma sha biyu.

Mai Martaba Sarkin Argungu, Alhaji Sama'ila Muhammad Mera a jawabin sa wurin taron, ya yabawa Gwamna bisa gudanar da wannan aikin a masarautar Argungu.

Haka kuma mai martaba Sarkin, ya zayyano wasu ayyukan cigaban da maigirma gwamnan ya gudanar a masarautar Argungu ciki har da bangaren ilimi da kuma irin taimakon da aka baiwa al'ummar da ambaliyar ruwa ya raba da muhallansu a jihar Kebbi inda Mai martaba yayi masa addu'ar cigaba da samun nasarori a gwamnatinsa.

Shugaban kamfanin da zai gudanar aikin, Dakta Hassan Mahadi yayi godiya ta musamman ga maigirma gwamna bisa aminta da yayi da su, ya ba su wannan damar domin su gudanar aikin.

Haka kuma yayi alkawarin kamfaninsu zai gudanar da aiki mai inganci kamar yadda aka bukata inda yace zasu kammala aikin cikin watanni shida (6 months) kafin wata goma sha biyu da aka baiwa aikin a hukumance. 

No comments