Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Nijeriya Za Ta Raba Wa Talakawa Miliyan 20 Tallafin Kuɗi

  Gwamnatin Najeriya ta ce tana shirin raba wa talakawan ƙasar guda 20 tallafin kuɗi domin rage musu raɗaɗin rayuwa. Ministan kuɗi da tattal...

 


Gwamnatin Najeriya ta ce tana shirin raba wa talakawan ƙasar guda 20 tallafin kuɗi domin rage musu raɗaɗin rayuwa.

Ministan kuɗi da tattalin arziki na Najeriya, Wale Edun ne ya bayyana haka a lokacin babban taron tattalin arzikin ƙasar karo na 30 a Abuja, babban birnin ƙasar.

Mista Edun ya ce gwamnatin za ta yi amfani da ribar da ta samu a watanni shidan farko na shekarar 2024 wajen raba tallafin, domin inganta rayuwar talakawan ƙasar da ke fama da matsin rayuwa.

A jawabinsa na bikin zagayowar ranar ƴancin kai na 1 ga watan Okotoba, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin ƙasar ta samu ribar naira tiriliyan 9.1 a watanni shidan farkon shekarar da muke ciki.

Adadin ya ninka abin da aka samu a shekarar da ta gabata, inda aka samu naira tiriliyan 4.06 a daidai irin wannan lokacin.

Ministan kuɗin ƙasar ya ce shirin zai shafi kashi 60 cikin 100 na talakawan ƙasar.

Mista Edun ya kuma jaddada ƙudurin gwamnatin ƙasar na mayar da hankali wajen inganta harkokin noma da masana'antu da albarkatun mn fetur da gidaje, waɗanda ya ce su ne manyan ɓangarorin tattalin arzikin ƙasar.

Abin da ya sa gwamnati za ta raba tallafin

Malam Abdulaziz Abdulaziz, ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban ƙasa Bola Tinubu ne, ya shaida wa BBC cewa tallafin wata hanya ce da gwamnatin ƙasar ta ɓullo da shi domin rage wa talakawa raɗaɗin da suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne dai Shugaba Tinubu ya sanar da matakin cire tallafin man fetur jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa, inda ya alƙawarta yin amfani da kuɗin tallafin man wajen raba wa talakawan ƙasar don rage musu raɗaɗin abin da hakan zai janyo musu.

Malam Abdulaziz ya ce a baya ana bai wa gidaje miliyan biyar tallafin, to amma ya ce a yanzu za a faɗaɗa shirin zuwa gidaje miliyan 20.

Ta yaya aka zaɓo mutanen da za su amfana da tallafin?

Malam Abdulaziz Abdulaziz ya ce an yi amfani da rajistar adana bayan talakwan ƙasar ne wajen zaɓo sunayen mutanen da suka cancani samun tallafin.

''A baya an yi ta samun matsaloli nan da can, inda a wasu lokuta ma tallafin ke ƙarewa a aljihun mutanen da ba su cancanta ba, wannan ne dalilin da ya sa a yanzu aka yi amfani da rajistar adana bayanan talakawan ƙasar domin kauce wa samun matsaloli'', in ji Malam Abdulaziz.

Ya ci gaba da cewa gwamnati ta kuma sake tantance sunayen da ke cikin rajistar domin kauce wa bayar da tallafin ga mutanen da ba su cancanta ba.

Nawa-nawa talakawan za su samu?

Gwamnatin ba ta yi ƙarin haske kan adadin kuɗin da kowane talaka cikin wadanda za a raba wa tallafin zai samu ba.

Amma a baya gwamnatin Shugaba Tinubu ta tsara cewa za ta riƙa biyan tallafin naira dubu takwas-takawas ga ƴan ƙasar, domin ganin kuɗin ya zagaya a tsakanin jama'a.

Tsawon lokacin da za a ɗauka ana bayar da tallafin

Haka nan kuma gwamnatin ba ta bayyana tsawon lokacin da za a ɗauka ana biyan tallafin ba.

Sai dai a baya gwamnatin ta ce za ta rabar da tallafi ga wasu talakawan ƙasar har na tswon wata shida.

No comments