Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijeriya A Shekaru 64: Ba Wani Abin Nunawa Da Samun 'Yancin Kai Idan Ba Yaudara Ba, In Ji Kuchi

Daga Awwal Umar Kontagora Wani matashin dan siyasa kuma dan jam'iyyar APC mai mulki, Hon. Zakari Muhammad Kuchi ya bayyana cewar batun s...

Daga Awwal Umar Kontagora

Wani matashin dan siyasa kuma dan jam'iyyar APC mai mulki, Hon. Zakari Muhammad Kuchi ya bayyana cewar batun samun 'yancin kan Nijeriya na shekaru 64 ba wani abin nunawa in ba yaudarar talakawan kasa da shugabanni ke yi ba.

Hon. Zakari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna fadar gwamnatin jihar Neja, inda ya ci gaba da cewar kasar da talaka bai da tabbacin samun abinci a yini sau uku a rana wani 'yanci take da shi da har za ta yi murna akai.

"Tun zuwan Janar Buhari akan mulki, har saukarsa zuwa kan shugaba Bola Ahmed Tinubu kullum talaka ana kan gasa masa aya a kumbarsa, mun ce PDP ta lalata komai, shekaru takwas na Buhari bai gyaru ba, yau Bola Ahmed Tinubu ya karba in ban da maganar hanyoyin samun haraji da karfafa guiwar masu arziki ba wani riba ko 'yancin da talakan kasar nan zai ce ya amfana da shi", in ji shi.

Ya ci gaba da cewa; a saboda haka, maganar bukukuwan ranar 'yancin kan Nijeriya na shekaru 64, yaran wasu yan amshin shata ne da ke cin gajiyar azabar da talakan kasar nan ke sha ke murna da shi.

Da ya juya kan jihar Neja kuwa, matashin ya ce lokaci da 'yan siyasa za mu fito mu fadawa gwamna gaskiya, domin lokaci ya wuce da yawa kuma a shekaru daya da doriya ba aiki daya da zamu nuna cewar gwamnatin nan ta shirya shi kuma ta kammala.

"Ka dauki maganar aikin hanyoyin da ake tada jijiyar wuya akan shi, ban da kara azabtar da talaka a jihar nan ba abin da aikin ya amfanar da talakan da aka ce ana yin aikin domin shi, sannan 'yan siyasar da suka wahala suka tallata jam'iyya da rokon Allah da lokacin su, gwamnatin nan ba kalle su ba, balle a saka masu saboda wahalar da suka yi", ya ce.

Ya ci gaba da cewa; yau abin takaici ma, ba wani mai rike da mukamin siyasa a jihar Neja, da zai iya buga gaba kan wata matsala ta al'umma ya yi gaba gadi wajen aiwatar da shi, saboda shi ma ta kan sa yake saboda halin da ya samu kan shi.

"anzu, bari in bada misali, a baya muna maganar wutan lantarki, yanzu za mu ana dan samun sa, amma kaso sittin na unguwanni a cikin garin minna ba su da wutan lantarki sakamakon lalacewar transformer na cikin unguwanni, ga misali daya Dutsen Kuran Gwari zuwa gidan gwamnatin jiha, bai wuce kilomita biyar ba, amma sama da watanni biyar zuwa shida ba wutan lantarki, kuma inda ya kamata su kai kukansu sun kai har yanzu ba a saurare su ba.

"Ina baiwa maigirma gwamna Hon. Umar Mohammed Bago shawara, kamar yadda Alla ya sahale masa, ya ba shi jihar a hannunsa sakamakon rashin yan siyasar da suka san me ake cewa siyasar, da zasu tsayu kan hakkin talakawa, da ya zauna ya dubi halin da talakawa ke ciki, ya canja tsarin tafiyarsa wajen bullo da gurabun hanyoyin dogaro da kai, ta yadda talaka zai samu saukin rayuwa.

"Amma, bayan tsadar rayuwar ma ko fita neman abinci na shrin gagarar talaka sakamakon farfashe hanyoyin da ake tayi a cikin jihar, domin inda abin hawa zai kai a jiya akan naira dari, yau zuwa da dawowa sai ka kashe dubu daya, kuma ba ka da tabbas akan idan ka fitan ma za ka samu.

"Tsarin siyasar, tsari ne na kyautata rayuwar al'umma, ta yadda al'umma zasu yi bugun gaba da abinda suka zaba, tsarin ilimi bai da alkibla, kiwon lafiya ma haka, gara idan kana da kudi daga makarantu har cibiyoyin kiwon lafiya ka zuyarci masu zaman kan su akan na gwamnati.

"A matsayina na dan APC da muka shiga lungu da sako wajen neman jama'a su mara mana baya, in har da gaske muna son dorewar jam'iyyar nan, ya kamata daga matakin kananan hukumomi, jiha da tarayya, mu waiwayi abinda ke faruwa dan gaggawar gyara kafin lokaci ya kure mana, amma don muna yayan jam'iyya ba za mu ga kurakurai mu kawar da idanu dan wasu daga cikin mu na cin moriya, idan kalilan na dariya dubbai na kuka to wani cigaba ke nan aka samu, ya zama rayuwar mai hakar rijiya, rami na kara zurfi amma yana ganin ya cigaba", ya karkare. 

No comments