Daga Hussaini Yero A yayin da ake bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun 'yanci daga turawan mulkin mallaka, Sanata Abdula...
Daga Hussaini Yero
A yayin da ake bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun 'yanci daga turawan mulkin mallaka, Sanata Abdulaziz Yari, mai wakiltar mazaɓar Zamfara ta yamma a Majalisar Dattawa ya jagoranci addu'ar samun nasara akan yaƙi da gwamnati ke yi da ƴan bindiga ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Tunibu Ahmad Tinubu.
A jawabinsa, Sanata Yari ya tabbatar da cewa babu wani biki da za su yi a yau wanda yawu ce addu'a don samun zaman lafiya, "kuma sakamakon halin da muke ciki na matsalar tsaro shekara da shekaru ya sa muka samu tawaya ta kowanne ɓangare na rayuwa", in ji Sanata Yari.
"Don haka ba mu da wani abin yi da ya wuce yi wa ƙasa addu'a a wannan lokacin bikin cika shekaru 64 don samun zaman lafiya", ya ce.
Sanata Yari ya ƙara da cewa, yima shugaban ƙasa Tinubu addu'a da jami'an tsaronmu a ko da yaushe zai taimaka wajen samun nasara ga waɗannan 'yan ta'adda da sulhu ya hamanta gare mu da su illa mu ga bayan su don samun ci gaban mu.
A nasa jawabin jagoran addu'a Malam Liman Dan Alhaji ya tabbatar da cewa, addu'a da Sanata Yari ke Jagoranta ba wannan bane na farko kuma koda yaushe yana tare da mu a jiki da ruhi wajen addu'a da ya ke ɗaukar nauyinta ba dare babu rana.
"Don haka idan mun koma garuruwan mu za mu ci gaba kamar yadda muka saba mun dai fara ganin nasara yanzu haka a Zamfara da jami'an tsaro ke samu wajen yaƙi da ƴan Bindiga", ya nusasshe.
No comments