Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƴan Shi'a sun tallafawa waɗanda Ambaliyar ruwa ya shafa da kayan abinci a Maiduguri

Ƴan uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky waɗanda aka fi sani da ƴan shi'a sun kai tallafin abinci a jihar Borno mus...


Ƴan uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky waɗanda aka fi sani da ƴan shi'a sun kai tallafin abinci a jihar Borno musamman ga waɗanda ambaliyar ruwa ya shafa a birnin Maiduguri. 

Wakilinmu da ya shaida lamarin, ya labarto cewa sun soma rabon tallafin ne a ranar Litinin 30 ga watan Satumban 2024 wanda suka ce za su kwashe tsawon mako guda suna wannan rabon. 

Kwamitin Maukibin Sayyada Zahara a ƙarkashin Jagorancin Shaikh Zakzaky ne suka gudanar da tallafin rabon abinci ga al'ummar da ibtila'in ya shafa. Kuma rabon ya kasance ne a Unguwannin da ambaliyar ruwan ya shafa. 
 
A zantawar wakilinmu da ɗaya daga cikin masu rabon abincin, Idris Muhammad Katusha ya tabbatar mana da cewa za su kwashe kwanaki bakwai suna rabon abincin. "Yau rana ce ta farko a cikin kwanakin da muka tanadar domin yin wannan aikin na alkhairi, kuma insha Allah za mu kwashe kwanaki bakwai muna yi", in ji shi.


Ya ci gaba da cewa, "wannan wani aikin jin ƙai ne da Jagoran Harkar Musulunci Sayyid Ibraheem Zakzaky ya saba gudanarwa. Kuma ana yin wannan ne domin sauƙaƙawa waɗanda wannan ambaliya ya shafa".

Wakilinmu ya tattauna da waɗanda suka amfana da wannan tallafin na abinci, inda suka nuna farin cikin su da jin daɗin su tare da fatan alheri ga Shehin Malamin bisa wannan tallafi da ya kawo musu.

No comments