Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya sanar da cewa gwamnatin Jihar za ta bai wa shigabannin makarantu tallafin naira 200,000 kowane wata dom...
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya sanar da cewa gwamnatin Jihar za ta bai wa shigabannin makarantu tallafin naira 200,000 kowane wata domin inganta ɓangaren ilimi a jihar.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook gwamnan ya bayyana cewa tallafin zai taimakawa shugananin makarntun wurin don aiwatar da sabbin shirye-shiryen ilimi, waɗanda za su haifar da ingantattun sakamako ga ɗalibai, da kuma ƙara kuzari da ɗabi'a a tsakanin ma'aikata.
Gwamna Aliyu ya ce ''Bayar da tallafin kuɗi ga shugabannin makarantu zai haɓaka kwarin gwiwarsu, tare da ƙarfafa su don ɗaukar nauyi mafi girma wajen haɓaka ingantaccen yanayin makaranta.''
Ya ƙara da cewa tallafin zai taimaka wurin haɓaka ƙwarewar ma'aikatan makaranta, wanda zai haifar da ingantattun malamai waɗanda za su iya ba da ilimi mai inganci.
''Ta hanyar mayar da hankali kan jagorancin makaranta, wannan yunƙurin yana ƙarfafa gwiwar al'umma wurin shiga a dama da su a harkar ilimi wanda zai haɓaka haɗin gwiwar da zai amfanar da ɗalibai da kuma makarantu.'' in ji shi
No comments