An ɗauki gomman shekaru ana tafka muhawara kan yadda siyasar Najeriya ke tafiya, inda wasu ke ganin kamar dimokuraɗiyyar ba ta cigaba yayin ...
An ɗauki gomman shekaru ana tafka muhawara kan yadda siyasar Najeriya ke tafiya, inda wasu ke ganin kamar dimokuraɗiyyar ba ta cigaba yayin da wasu ke cewa lallai kwalliya tana biyan kuɗin sabulu.
Bishop Mathew Hassan Kukah na cikin waɗanda ke ganin siyasar ƙasar na cike da matsaloli, inda ya ce duk da cewa siyasar ƙasar ta faro da kyau daga bisani, musamman tun bayan fara juyin mulki da sojoji suka yi, dimokuraɗiyyar ƙasar ta fara samun tangarɗa.
A tattaunawarsa da BBC, Bishop Kukah wanda jagoran Cocin Katolika ne a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, ya ce ba siyasa kaɗai ba "duk wani abu da ake so ya yi kyau dole sai an ɗora shi a tubali mai ƙarko".
A ƙarshen makon jiya ne Bishop Kukah ya gabatar da wata lacac a Abuja, inda ya bayyana cewa yawancin shugabannin Najeriya na samun damar hawa karagar mulki ne ba tare da sun shirya mulkin ba, lamarin da ya jawo masa martani daga fadar shugaban Najeriya.
'Abin da aka shuka ake girba yanzu'
Bishop Kuka ya bayyana cewa ba a ɗora siyasar Najeriya a kan tubali mai inganci ba, wanda a cewarsa hakan ya sa domokuraɗiyyar ƙasar take cikin matsaloli masu yawan gaske.
"Gini sai an yi masa tubali mai kyau, idan ba a yi tubali mai ƙarko yadda ya kamata ba za a samu matsala," in ji shi.
"Dimokuraɗiyyar Najeriya ba mu samu tubali mai kyau ba. Kodayake mun fara siyasa a ƙasar da kyau, amma da a ce mun ci gaba tun daga lokacin su Sardauna - da sojoji ba su dagula ƙasar ba - da siyasar Najeriya ta zama daban."
Ya ƙara da cewa ai "abin da ake girba a yanzu shuka ce da aka yi a baya ta rashin ɗora
Manyan matsaloli

Duk da cewa siyasar Najeriya ta girma, kuma ta daɗe idan aka lissafa tun daga jamhuriya ta ɗaya, wasu na ganin har yanzu siyasar ƙasar cike take da matsaloli.
Bishop Kukah ya lissafo wasu matsaloli da ya ce suna cikin abubuwan da suka dabaibaye siyasar ƙasar tare da yi mata tarnaƙi.
"Idan mutane na cikin yunwa, suna cikin matsaloli daban-daban, ga kuma duhun kai, ga shi babu ilimi, ga mutane barkatai. Shi ya sa siyasar Najeriya ta zama mai wahala."
- Hawa mulki ba tare da shiri ba
A game da batun da ake yi cewa yawancin shugabannin Najeriya na hawa karagar mulki ne ba tare da sun shirya ba, babban malamin cocin ya ce haka siyasar Najeriya ta gada.
"Haka tarihin siyasar Najeriya yake," a cewarsa. "Muhammadu Bello (Sardauna) ne ya kamata ya zama firaiminista amma ya kira Abubakar Tafawa Ɓalewa, kuma ya yi aiki mai kyau. Amma bayan wannan sai muka shiga mulkin sojoji, inda ya zama duk wanda ke da bindiga shi zai yi mulki.
"Tsohon shugaban ƙasa Shehu Shagari sanata ya so ya zama, amma ya zama shugaban ƙasa. Olusegun Obasanjo daga kurkuku aka ɗauko shi.
"Goodluck Jonathan ya yi mataimakin gwamna, bai ma san zai zama gwamna ba, sai ga yadda abubuwa suka zama. Ko Umar Musa Yarduwa ma ya riga ya tsara zai koma ya ci gaba da koyarwa a jami’a ne kafin ya zama shugaban ƙasa."
- Bai wa matasa dama
Matasan Najeriya sun sha kokawa cewa ba a ba su damarmakin kamar yadda ake ba takwarorinsu a ƙasashen waje.
Sai dai Bishop Kukah ya ce siyasa batu ne na kuɗi, amma ya ƙara da cewa kowa shugaba ne a matakin da yake.
"Ba kowane mutum ne zai zama shugaba mai riƙe da mulki ba. Idan kana da iyali kai shugaba ne. A duk inda kake aiki kai shugaba ne. Idan ana maganar shugabanci, mutanen Najeriya suna ganin shugaba shi ne mai mulki. Waɗannan suna riƙe da madafun iko ne. Gyara Najeriya ba aikin masu mulki ba ne kawai, kowa na da rawar da zai taka a matakin da yake.
"Idan aka ce yara manyan gobe ya danganta ne da abin da Allah ya ba mutum. Ko gadi kake yi, to ka yi yadda ya kamata. Ƴansiyasa na aikinsu daban, ƴankasuwa na nasu, kowa na nasa. Idan kowa ya yi aikinsa da gaskiya Najeriya za ta gyaru, duniya ma za ta gyaru."
- Haɗama
Bisa al'ada a siyasar Najeriya, akasarin masu mulki kan so su kai har magaryar tuƙewa.
Malamin cocin ya ce dole ne mutane su gane cewa siyasa na buƙatar haƙuri, da sauƙin kai - ba handama ba.
A cewarsa: "Kansila yana so ya zama shugaban ƙaramar hukuma, shugaban ƙaramar hukuma yana so ya zama gwamna, gwamna yana so ya zama shugaban ƙasa - idan bai samu ba yana so ya zama sanata.
"Shi ya sa majalisar dattawan Najeriya take cike da tsofaffin gwamnoni."
No comments