Jagoran jam'iyyar NNPP na jihar Borno, Attom Muhammad Magira ya ajiye muƙaminsa na jagorancin jam'iyyar, da ma jagorancin ƙungiyar K...
Jagoran jam'iyyar NNPP na jihar Borno, Attom Muhammad Magira ya ajiye muƙaminsa na jagorancin jam'iyyar, da ma jagorancin ƙungiyar Kwankwasiyya ta jihar.
A wata wasiƙa da ya rubuta zuwa shugaban jam’iyyar NNPP na mazaɓarsa ta Gwanje I, Magira ya ce, “ni Attom Muhammad Magira na ajiye muƙamin jagoran jam’iyyar NNPP a jihar nan da kuma ƙungiyar Kwankwasiyya movement a jihar Borno daga ranar 25 ga Nuwamban 2024.
"Ina godiya da goyon bayan da mutanen Borno suka ba ni, kuma ina godiya da goyon bayan da na samu daga babban madugun NNPP, Injniya Rabiu Musa Kwanwaso."
No comments