Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kebbi Ta Ɗauki Nauyin Gasar Karatun Ƙur'ani Ta Shekarar 2024

Jihar Kebbi  ta  dauki nauyin gasar karatun Al'kur'ani ta shekarar 2024 da aka shirya gudanarwa daga ranar 19 zuwa 27 na watan Disam...



Jihar Kebbi  ta  dauki nauyin gasar karatun Al'kur'ani ta shekarar 2024 da aka shirya gudanarwa daga ranar 19 zuwa 27 na watan Disamba wanda dukkan jihohin Nijeriya ke halarta, jami'ar Usman Danfodiyo ne ke shiryawa kowace shekara.

Babban kwamitin da gwamnati ta kafa wanda ya kunshi malaman musulunci da jami'a da ma'aikatan gwamnati karkashin jagorancin Sarkin Argungu Alhaji Sama'ila Muhammadu Mera sun gudanar zama na farko a fadar Sarkin ranar litinin data gabata don fara shirin yadda za a samu nasara ga nauyin da gwamnati ta daura musu. 

Sarkin ya tunatar da mambobin kwamitin aikin da ke gabansu don haka ya yi kira gare su da su sadaukar da kansu domin samun nasarar aikin.

"Ina godewa Gwamna Kebbi Nasir Idris kan nada mu da ya yi ga aikin daukaka Al'kur'ani da addini."

"Muna da babban aiki a gabanmu, muna godewa Allah da ya yi mu musulmai karkashin karanatarwa Annabin rahama Muhammad(S.A.W), abin farinciki ne gare mu na samun satin daya ana karanta Kur'ani jihar mu, yakamata mambobin kwamiti ku sani mutane ne za su zo daga kowane bangare a Nijeriya don haka mu yi aikin mu da tsoron Allah."

"Ina da yakinin za mu gudanar da gasar cikin tsari don haka muke gayyatar al'umma su halarci Musabakar da za a soma ranar 19 a kammala 27 ga watan Disamban 2024."


No comments