Daga Hussaini Yero Uwargidan Gwamnan Zamfara Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana takaicin ta kan yadda ake samu Jami'an tsaro da laifin cin ...
Daga Hussaini Yero
Uwargidan Gwamnan Zamfara Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana takaicin ta kan yadda ake samu Jami'an tsaro da laifin cin zarafin mata wato fyade,akan haka ta yi kira ga mahukunta da su sanya duk jami'an tsaro da aka kama da cin zarafin mata a kafafen yada labarai kamar yadda suke gabatar da masu laifi ga 'yan gidan Talabijin da Rediyo da jaridu domin ya zamo izina ga sauran jami'an tsaro.
Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana hakan ne a ranar Laraba rana ta uku na yaki da cin zarafin mata wanda aka yi ma fyade da marasa galihu da ake tauye ma hakkokin su a Gusau babban birnin jihar.
A jawabin ta Huriyya Dauda ta bayyana cewa a jawaban da aka gudanar a yanzu ya tabbatar da cewa, fitatun mutanene kuma sanannu ake kamawa da laifin cin zarafin mata a don haka muka kaddamar da kwamitoci a kananan Hukumomi domin yaki da masu aikata wannan mumunan laifi dan kawo karshen su.
"Kuma yau ga littafai nan na turancin mun fasara su zuwa Hausa zamu raba domin mutane su gane illar cin zarafin mata da kuma hukuncin da mai yi zai gamu da shi", in ji ta.
Hajiya Huriyya ta kara da cewa, ba fyade bane kade cin zarafin mata akwai rashin ba su hakkin su na kulawa ga mazajen su na rashin abinci da karatun 'ya'ya mata da sauran su.
"A don haka doka za ta yi aiki akan duk wanda aka kama a Zamfara wadannan munana lafiya", inji Huriyya Dauda.
"Kuma muna godiya ga Kwamishin Kananan Hukumomi da masarautu Hon. Ahmad Yandi ya bayyana cewa, ma'aikatar kananan Hukumomi za su yi hadin guiwa da Sarakunan mu goma sha tara wajen yaki da masu wannan mumunan laifi. Kuma zamu dauki nauyin kara litatafan domin shigar da su ko'ina a fadin jihar ta Zamfara".
No comments