Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NUMW, MAN Sun Nuna Takaicinsu Da Kamen Da Hukumar EFCC Ta Yi Wa Leburorin Hakar Ma'adanan Kasa A Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Hadakar kungiyoyin kwadago na masu hakar ma'adanan kasa ta Nijeriya wato 'Nigeria Union Of Mine Workers da...


Daga Awwal Umar Kontagora

Hadakar kungiyoyin kwadago na masu hakar ma'adanan kasa ta Nijeriya wato 'Nigeria Union Of Mine Workers da Miners Association of Nigeria' reshen jihar Neja,  sun nuna takaicinsu kan kamen da hukumar EFCC taiwa leburorin ma'adanai a jihar Neja.

Bayanin na kunshe ne a wata ganawar hadin guiwa da kungiyoyin su kayi da manema labarai yammacin larabar makon nan a Minna.

Tunda farko a bayaninsa,shugaban riko na kungiyar MAN, Hon. Yusuf Shu'aibu Mami Suleja,  ya ce abin ya wuce hankali,  domin babu wani hurumin doka da ya baiwa EFCC shiga hurumin ma'aikatan ma'adanan kasa,  da har zasu kutso daga jihar Kaduna su shigo Neja su kama leburorin ma'adanan kasa,  mu a dukkan tafiyar kungiyoyin nan biyu muna da takardar amincewa daga gwamnatin tarayya,  muna gudanar da ayyukan mu ne akan doka. Sannan gwamnatin jiha ta kafa kwamitin sanya idanu kan hana aikin ma'adani ba bisa ka'ida ba,  bisa jagorancin sakataren gwamnatin jiha wanda wannan kwamitin tana kan aikinta.

Kan haka mun rubuta takardun korafi zuwa ga ministan kula da ma'adanan kasa na tarayya,  mun rubutawa shugaban rungumar yan sanda ta kasa,  kuma mun rubutawa sakatariyar MAN da NUMW ta kasa kuma mun rubutawa ma'aikatar kula da ma'adanan kasa ta jihar da dukkanin hukumomin da abin ya shafa.

Ni kaina ranar larabar da ta gabata EFCC ta gayyace ni a Kaduna kuma na tafi sun min tambayoyi,  da farko ma muna zargin cewar ko akwai wasu kudaden gwamnati da aka yi ruf da ciki da sune aka shigo da su wajen yan ma'adani, amsar da suka ba ni wai suna zargin wadanda suka kama da aikin ma'adani ba bisa ka'ida ba, shi wace doka ko kundin tsarin mulki ya baiwa EFCC damar shiga bangaren ma'adani.

Saboda haka wajibi ne duk hanyoyin da suka kamata mu bi wajen dakatar da wannan kutsen mu tabbatar mun bi shi,  saboda muna gudanar da ayyukan mu bisa tsari da dokokin kasar nan.

" Mun ji cewar wasu suna kiran taro suna karbar kudade hannun mutane musamman yan uwan wadanda da aka kama da sunan beli,  tun da nazo kan kujerar nan ban karbi kudi hannun kowa ba,  wannan abinda ake yi ba hannun MAN balle NUMW a cikin shi.

A na shi bangaren kuwa,  Comr. Musa Adamu Nasko,  shugaban kungiyar leburori masu hakar ma'adanan kasa  ( NUMW), yace da farko EFCC ta kama mutane ashirin da biyu ta tafi da su Kaduna,  mun binciki rundunar yan sanda ta jiha,  ta tabbatar mana ba ta san da zuwan EFCC ba,  mun binciki hukumar DSS sun tabbatar mana ba su san da kamen ba.

Ganin haka yasa muka gaggauta sanar da gwamnatin jiha,  da hukumomin da abin ya shafa a jihar Neja,  bayan nan mun tura lauyoyin zuwa shalkwatan EFCC da ke Kaduna,  da farko sun ce zasu kai su kotu,  mun amince da a tafi kotu din,  domin wadanda aka kama wasun su ko asusun ajiya ba su da shi a banki,  balle a zarge su da amsar kudaden wasu batagari su boye,  da yawan su mutane ne da sai sun fito sun yi leburanci su samu abin ciyar da iyalan su.

Wani abin daure kai ba ma a daji aka kama su ba, suna aiki ne akan injinan da ke tace kasar da aka hako,  da aikin su ke son yi na kame ba mutane da ke cikin gari zasu farauta ba,  su shiga daji su ga abinda zai faru.

Zuwa yanzu bayan kamen farko na mutane ashirin da biyu,  sun sake kutsowa sun kama mutane ashirin da hudu, yanzu muna da mutane arba'in da hudu a hannun su.

Jiya talata kuma sai ga sakon kartakwana na wayar hannu wai suna gayyatar wasu mutane goma sha daya a Kaduna.

Wajibi ne gwamnati ta dakatar da EFCC wannan kutsen akan hurumin da bai shafe ta ba,  ba zamu lamunci irin wannan cin zarafin ba,  dukkanin mambobin mu daga kan yan kasuwa da leburori suna da rajista kamar yadda gwamnati ta umurta mu yi,  hukumomin da alhakin kula da harkar ma'adani ke hannunsu daga ma'aikatar kula da ma'adanai na tarayya da jiha da hukumomin tsaro muna aiki da su kafada da kafada dan muna da kyakkyawar fahimta juna ta aiki.

Amma ba wani hurumin dokar da tace mu yi aiki da EFCC dan aikin mu bai da alaka da yin almundahana da kudaden gwamnati,  mu yan kasuwa ne da ke nema da kafin bisa tsarin dokokin kasar mu.

Muna kiran gwamnatin jiha da babban murya da ta tabbatar ta binciko wadanda ke da hannun akan wannan aika-aikar da samun mafaka ga hukumar EFCC har suna tatsar mutane kudade da sunan beli,  duk ayyukan da muke gabatarwa a cikin aljihun kungiyoyin muke fitar da su ba ma labewa change and bill da sunan shiga tsakani.  Kawai mun fahimci wasu ke labewa da rigar siyasa suna yiwa gwamnati zagon kasa da kokarin bata mana suna. 


No comments