Daga Awwal Umar Kontagora Ma’aikatar Kula da Harkokin Makiyaya da Manoma Mayawata ta Jihar Neja ta kaddamar da shirin tattara ...
Daga Awwal Umar Kontagora
Ma’aikatar Kula da Harkokin Makiyaya da Manoma Mayawata ta Jihar Neja ta kaddamar da shirin tattara bayanai kan al’ummar makiyaya. Wannan shiri na musamman na farko ne wanda zai zama tubali wajen samar da tsare-tsaren ci gaba da suka shafi wadannan al’ummomi.
Kaddamarwar ta gudana a kananan hukumomi uku: Bosso, Chanchaga, da Paikoro, tare da nufin wayar da kan al’umma game da mahimmancin shirin da kuma share fagen tattara cikakku kuma amintattun bayanai kan al'ummar makiyaya a makonni masu zuwa, wanda zai hada da masu kula da aikin da kuma masu tara bayanan.
Taron farko ya gudana a hedikwatar karamar hukumar Bosso da ke Maikunkele, inda Kwamishinan Ma’aikatar, Hon. Umar Ahmed Sanda Rebe, ya yi bayanai kan muhimmancin samun ingantattun bayanai don magance kalubale na musamman da ke fuskantar al’ummar makiyaya. Ya ce: “Wannan kaddamarwa ba kawai taro ba ce, sai dai wata hanya ce ta bude kofar ci gaba mai ma’ana ga al'ummar makiyaya.”
Shugabar karamar hukumar Bosso, Hon. Ladidi Bawa Bosso, ta tabbatar da cikakken goyon bayanta ga wannan shiri, tana mai bayyana kwarin gwiwarta kan nasarorin da za a cimma.
Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Salihu Muhammad Alfa, ya halarci taron tare da manyan jiga-jigan masu ruwa da tsaki da shuwagabannin Makiyaya kamar Ardo Sama’ila Rebe da Ardo Muhammad Guddel, da kuma shugabannin gargajiya daga bangarorin manoma da makiyaya, wadanda suka bayar da gudunmawa wajen bayyana mahimmancin shirin.
A Chanchaga, an gudanar da taron wayar da kai a hedikwatar karamar hukumar ita ma, inda Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Aminu Ladan ya samu wakilcin sakataren karamar hukumar. Kwamishinan Nomadic ya sake jaddada muhimmancin hadin kan al’umma wajen tabbatar da nasarar wannan shiri.
Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Sarkin Fulani Tukur, Ardo Sama’ila Rebe, Ardo Muhammad Guddel, da wasu ma’aikatan Ma’aikatar Kula da Harkokin Makiyaya.
Wuri na karshe na taron ya kasance a karamar hukumar Paikoro, inda mahalarta taron suka nuna gagarumin goyon baya. Shugaban karamar hukumar, Hon. Umaru Aminu Yandayi, ya yaba wa Ma’aikatar bisa wannan tsari na zamani na shigar da makiyaya cikin shirye-shiryen ci gaban al’umma.
Ardon Paikoro, Alhaji Hussaini Yusuf Bosso, yana daga cikin wadanda suka halarci taron tare da Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Salihu Muhammad Alfa, da sauran manyan ma'aikatan Ma'aikatar Nomadic da suka rufawa Kwamishinan baya da masu ruwa da tsaki.
Wannan kaddamarwa ta share hanya don fara aikin tattara bayanai nagartattu, wanda za a soma nan ba da jimawa ba tare da hadin gwiwar masu kula da aikin da masu tara bayanai.
No comments