Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masarautar Koko Ta Zama Ta Farko A Bikin Tunawa Da Al'adun Gargajiya Da Masarautar Gwandu Ta Shirya

Daga Awwal Umar Kontagora Masarautar gundumar Koko da ke karkashin masarautar Gwandu ta jihar Kebbi ta zama ta farko da ta kayatar a bukin t...



Daga Awwal Umar Kontagora

Masarautar gundumar Koko da ke karkashin masarautar Gwandu ta jihar Kebbi ta zama ta farko da ta kayatar a bukin tunawa da al'adun gargajiya da masarautar Gwandu ta shirya.

Tunda farko da yake jawabi bisa wannan gagarumin rinjayen,  Sarkin Koko na shida,  Muhammadu Bello Koko II,  ya yabawa al'ummar gundumar Koko bisa hadin kai da bada goyon baya wajen ganin masarautar Koko ta fito da wannan kambu iirinsa na farko tun kafuwar gundumar Koko.

Sarki Muhammadu Bello Koko II, ya jawo hankalin yan asalin garin da su cigaba da baiwa gwamnatin Kwamred Nasiru Kauran Gwandu duba da irin salon mulkinsa na cigaban jihar Kebbi da al'umma baki daya,  yace wannan nasarar bukin baje kolin gargajiya da masarautar Gwandu ta samu ya biyo bayan jajircewar maigirma gwamna Kwamred Nasiru Kauran Gwandu na farfado da darajar al'adun gargajiya a jihar Kebbi,  wanda hakan zai samar da cigaba ta fuskar zamantakewa,  kasuwanci,  noma da kiwo da dorewar zumunci tsakanin al'ummar masarautar Gwandu da jihar Kebbi baki daya.

Sarkin ya hori matasa da su zama masu kishin kan su wajen rungumar karatun boko da na addini,  kasuwanci,  noma da muka gada iyaye da kakanni.

A bayaninsa,  shugaban kwamitin shirya bukin na al'adun gargajiya,  Muhammad Bashir Abdullahi Firchin Koko,  ya yabawa yan kwamitinsa da Sarkin Koko ya dora ma alhakin jagorantar gundumar Koko,  wanda hadin kan da suka bayar ne ya ba su wannan gagarumin nasara.

Hakan,  ya nuna cewar lallai al'ummar Koko suna bukatar cigaba fiye da yadda aka san su.

Dan haka za mu cigaba da lalubo duk wata hanyar da za ta ciyar da garin Koko gaba,  za mu yi anfani da matsayin mu da duk wata hanyar da muka samu dama dan ganin al'ummar Koko sun anfana.

Gundumar Koko na cikin karamar hukumar Koko-Besse ta jihar Kebbi,  wadda ta shahara wajen noma da kiwo,  kasuwanci da ilimin zamani da na addini.

Sarki Muhammadu Bello Koko II,  shi ne sarkin Koko na shida da yazo a wannan karnin. Matashi ne cikakken dan boko mai kwarewa da sanin makamar aiki,  wanda al'umma da dama ke da yakinin zamansa a wannan kujerar zai yi tsayin daka wajen ganin ya samar da nasarori masu alfanu ga al'ummar Koko. 


No comments