Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Shugabannin Siyasar Sakkwato Su Yi Koyi Da Jihar Kebbi

Daga Awwal Umar Kontagora Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar yayi kira ga yan siyasar jihar Sokoto da su yi koyi da yan s...



Daga Awwal Umar Kontagora

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar yayi kira ga yan siyasar jihar Sokoto da su yi koyi da yan siyasar jihar Kebbi,  Sarkin musulmi yayi wannan kiran ne ganin yadda ya ga tsoffin gwamnonin jihar Kebbi suka zauna kusa da juna har da gwamna ma ici cikin farin ciki da raha da juna a lokacin bukin al'adun gargajiya na masarautar Gwandu.

Sarkin Musulmi ya bayyana jin daÉ—insa akan hakan inda yayi kira da za'a a samu irin wannan haÉ—in kai da siyasa mai tsafta irin wannan da ya gani ga shugabannin siyasar jihar Kebbi.

Sarkin Musulmin ya bayyana wannan haɗin kai da ya gani tsakanin tsoffin gwamnonin Kebbi a matsayin abin koyi kuma abin alfahari inda yace duk da banbancin siyasa ko jam'iyya bai hana gwamnoni haɗuwa wurin ɗaya ba domin cigaban al'ummar Jiharsu da kuma haɓaka irin kokarin Malam Abdullahi Fodiyo a jihar da yayi a baya.

Sa'ad Abubakar yayi wannan kiran ne a garin Birnin Kebbi a lokacin gabatar da wata Æ™asida akan rayuwar Malam Abdullahi Fodiyo da aka gudanar a masaukin shugaban Æ™asa da ke garin Birnin Kebbi a wani É“angare na bikin wasan al'adun gargajiyar masarautar Gwandu. 

No comments