Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar SERAP ta buƙaci Tinubu ya bincika zargin badaƙala a ma'aikatar jinƙai

Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya, ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da ya gudanar da binciken kuɗi sama da ...



Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya, ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da ya gudanar da binciken kuɗi sama da naira biliyan 57 da ake zargin an sace ko sun ɓace daga ma’aikatar jinƙai da yaƙi da fatara ta tarayya a shekarar 2021.

A cewar SERAP, binciken ya zama dole domin wanke gwamnatin tarayya daga zargin ɓoye masu aikata laifuka.

Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen jin ƙai a sassa daban-daban na Najeriya.

No comments