Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa akalla ‘yan Nijeriya 10,000 ne aka tsare bisa laifukan shige da fice a kasashen Af...
Mataimakin shugaban
kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa akalla ‘yan Nijeriya 10,000 ne aka tsare
bisa laifukan shige da fice a kasashen Afirka da kasashen Turai a bana.
Sai dai ya yaba da
irin gudunmawar da baki ‘yan Nijeriya ke bayarwa ga tattalin arzikin duniya,
inda ya ce Nijeriya ce ke kan gaba a duk wani nau’in kudaden da ‘yan kasashen
waje ke aikawa da su a yammacin Afirka.
Baya ga kudaden da
ake aikewa daga kasashen waje, ya ce ‘yan Nijeriya dake zama a kasashen waje
sun zama jakadu nagari wadanda suka yi fice a fannin fasaha, likitanci,
wasanni, fasahar kere-kere, da sauran ayyukan da suka shafi al’umma.
Mataimakin shugaban
kasar ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin a yayin taron shekara-shekara na
‘yan ci-rani karo na 10 na kasa mai taken, “Beyond Borders: Celebrating
Migrant’ Legacy, Protecting their Rights,” a dakin taro na Banquet na fadar
shugaban kasa, a birnin Tarayya Abuja.
No comments