Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Bago Ya Yi Sulhu Da Ƴan Bindiga Don A Samu Zaman Lafiya

  Daga Awwal Umar Kontagora   An shawarci gwamnan Neja,  Babban manomin jiha,  Umaru Mohammed Bago da yayi sulhu da yan bindiga ...

 

Daga Awwal Umar Kontagora 

An shawarci gwamnan Neja,  Babban manomin jiha,  Umaru Mohammed Bago da yayi sulhu da yan bindiga kamar yadda takwaransa na jihar Kaduna Uba Sani yayi dan a samu zaman lafiya. 

Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki daga yankin Neja ta Arewa,  Alhaji Muhammad Lawal Hamdala Rijau yayi kiran labaran makon nan a Minna. 

Hamdala,  ya cigaba da cewar maganar gaskiya gwamna Umaru Bago ya dauko hanyar ciyar da al'umma da jihar gaba,  musamman wajen dawo da martabar harkar noma da ayyukan raya kasa da ya sanya a gaba,  amma matsalar tsaro ya hana al'ummomin karkara sakewa duk da cewar matakan da yake dauka yanzu matsalar tayi sauki sosai ba kamar shekarar da ya gabata ba. 

Salon mai girma gwamna na ziyarar yankunan kananan hukumomi da yake yi a halin yanzu zai taimakawa gwamnatin sa wajen sanin matsaloli da bukatun talakawa ta yadda zai samu saukin walwale su cikin sauki. 

Dan siyasar ya cigaba da cewar ko bayan kammala wannan ziyarar gani da ido da ke gudana a halin yanzu,  akwai bukatar Umaru Bago da ya cigaba da irin wannan ziyarar lokaci zuwa lokaci hakan zai bada damar sanya idanu akan ayyukan da gwamnatin ta sanya a gaba.

Muna da kyakkyawar zaton wannan hanyar da gwamnatin ta dauka mai bullewa ce, idan jama'a su kayi hakuri suka baiwa gwamnatin goyon baya,  jihar nan za ta tserewa tsara a fagen cigaba da bunkasar tattalin arziki. Amma ina jaddada cewar akwai bukatar bin duk wata hanyar samun zaman lafiya,  wanda zai saukaka kwararar jama'a cikin birane saboda matsalar tsaro,  dan haka sulhu alheri ne,  ya kamata adalin gwamnan mu ya jaraba hanyar sulhu musamman ganin yadda ya samar da kulawa da jin dadin manoma da makiyaya dan wannan ma'aikatar ta samu damar gudanar da ayyukan da zasu anfnani manoma da makiyayan jihar nan. 
Hamdala,  ya yabawa jagorancin shugaban jam'iyyar APC na jihar Neja,  Hon. Aminu Bobi bisa hanyoyin da yake bi wajen sulhuntawa da rigingimun cikin gida da kan taso nan da can wanda hakan yasa jam'iyyar APC ta zamo tsintsiya madaurin ki daya a jihar Neja.

No comments