Daga Awwal Jibrin Ƴankara A ranar Talata 3/12/2024 mai girma Sarkin Yamman Katsina Injiniya Alhaji Aminu Tukur Usman Saidu, Haki...
Daga Awwal Jibrin Ƴankara
A ranar Talata 3/12/2024 mai girma Sarkin Yamman Katsina Injiniya Alhaji Aminu Tukur Usman Saidu, Hakimin Faskari ya naɗa Malam Rabiu Yahaya (Information) Sakataren yaɗa labarai na ƙaramar Hukumar Faskari ta jihar Katsina a matsayin mai Unguwar a Unguwar Tudun Markabu daje cikin garin Faskari a jihar Katsina.
Sarkin Yamman Katsina ya naɗa Malam Rabiu Yahaya (Information) bisa cancantarsa da gogewar sa duk da bai gaji sarautar ba, amma saboda iya mu'amalarsa da haƙuri da al'umma aka ga ya cancanta a naɗa shi a wannan matsayin na Mai Unguwa.
Bayan kammala naɗin mai Unguwar Malam Rabi'u Yahaya ya Ggode ma Hakimin Faskari bisa wanna naɗi da ya yi ma su, kuma ya yi kira ga al'umma da su yi ƙoƙari a yi ma juna adalci da su da masu mulkin.
No comments