Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Sami Sabbin Naɗe-naɗe A Fadar Sarkin Yamman Katsina, Hakimin Faskari

Daga Awwal Jibril 'Yankara A  ranar Talata 3/12/2024, Sarkin Yamman Katsina Injiniya Alh. Aminu Tukur Usman Saidu Faskari, H...



Daga Awwal Jibril 'Yankara

A  ranar Talata 3/12/2024, Sarkin Yamman Katsina Injiniya Alh. Aminu Tukur Usman Saidu Faskari, Hakimin Faskari ya naɗa masu Unguwanni har guda goma a fadarsa da ke cikin garin Faskari ta jihar Katsina. 

Naɗin na masu Unguwanni ya biyo bayan rasuwar tsaffin masu riƙe da Unguwannin ne shiya sa aka naɗa makwafin waɗanda aka rasa. 

Masu Unguwani da aka naɗa sun haɗa da: 


1. Mal Rabi'u Mai Unguwar  Tudun Markabu. 
2. Mustapha Muhammad Mai Unguwar Zamfara. 
3. Malam Adamu Mai Unguwar Kogon Kura. 
4. Malam Sagir Ahmad Mau Unguwar Danzagi. 
5. Abdullah Tambai Mai Unguwar Ung. Dan Boka.

SAURAN SUN HADA ƊA: 

6. Mamuda Haruna Mai Unguwar Nasarawa ta Kudu. 
7. Alhaji Umaru Husaini Mai Unguwar Dan Maural
8. Abubakar Abdullah Mai Unguwar Kadisau ta Kudu
9. Lawal Sabo Mai Unguwar Bakin Kasuwa Faskari
10. Malam Samaila Ado Mai Unguwar Ung. Dudu

Bayan kammala naɗin Sarkin Yamman Katsina Injiniya Alh Aminu Tukur Usman Saidu Faskari, Hakimin Faskari ya yi kira ga masu Unguwanni da su ji ysoran Allah kuma su sani zalunci haramun ne kuma su yi ƙoƙari su riƙe amanar talakawan su, dmin muƙamin Mai Unguwa ba fa ƙaramin muƙamin ba ne.

Domin duk wani abu da ake son cimmawa to da ga gare su ake farowa.

Sannan Hakimin Faskari ya hori sabbin masu Unguwanni da ka da su yi wasa da sana'o'in su da suka yi su riƙe sana'o'in su sosai.

"Ko ni da kuka gani a wannan jujerar ba na wasa da kasuwanci. Domin shi ne za ku rufa ma kan ku asiri. Ba sai kun matsa ma waɗanda kuke shugabanta ba.

"Sannan ku sani bana nada ku bane don ku rinƙa amso kuɗi kuna kawo min, a'a ina da sana'a. Ni bana aika wa a amso min kuɗi wajen kowa kuma a don haka ba zan aiko kowa zuwa gare ku ba", in ji shi.

Ɗaya daga cikin masu Unguwanni da yake godiya a madadin sauran ya gode ma Hakimin bisa namijin ƙoƙarin da ya yi wajen naɗa masu sarautu a gidajen su bayan rasuwar mahaifan su, kuma za su yi iya iyawar su wajen kawo ci gaba a masarautun na su.

Shima a nasa jawabin Sakataren Sarkin Yamman Katsina Malam Hamisu Faskari, ya gode ma Hakimin bisa namijin ƙoƙarin da ya yi na ba su cikakkiyar dama wajen gudanar da aikin Masarautar. 

Haka zalika ya gode ma gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda bisa kula da yake yi da masu Unguwanni na ba su naira dubu goma duk wata. 

No comments