Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sabuwar Dokar Haraji: Yunkuri Ne Na Talautar Da Talakan Arewa Da ‘Yan Majalisar Tarayyar Mu Suka Karbo - Alhaji Awaisu

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar turkaturkar da yan majalisun dokokin tarayya ke ciki na ganin sun dadawa shugaban kasa Bola Ahmad...



Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar turkaturkar da yan majalisun dokokin tarayya ke ciki na ganin sun dadawa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu suna kokarin kammala kwangilar da suka karba ne dan cin ma burin shugaban kasar.  Wani dattijo mai fashin bakin harkokin yau da kullum,  Alhaji Awaisu Muhammad Giwa Wana ne ya bayyana hakan a yammacin lahadin makon da ya kare a Minna.

Awaisu Wana,  ya cigaba da cewar indai ba shugaba Tinubu na da wata boyayyar manufa na ganin bayan yankin Arewa da tattalin arzikinta ke cikin wani halin rai kwa-kwai,  mutu kwa-kwai ba,  ina maganar wannan sabon dokar zai haifarwa yankin da mai ido.

Su kan su yan majalisun tarayyar da ke rawar kafar ganin an yi dokar daman ba al'umma suke wakilta ba,  suna wakiltar kan su ne da iyalansu.  Sanin kowa ne tsadar rayuwa da talakan kasar nan ke ciki,  ga tsadar man fetur, abinci da sauran muhimman abubuwa su ko a jikinsu.

Amma ina jawo hankalinsu da su sani arewa wando ce,  duk wanda ya saka ya tube zai sake dawowa dan rufe al'aurarsa,  saboda haka talaka ya sani bai da shugaba a arewa dan haka kar wani ya fito gobe yana mai babatu a kafafen yada labarai yaudara ne .

Dattijon,  ya yabawa gwamnan Barno,  Farfesa Zulum,  kan fitowa da yayi ya bayyanawa duniya irin jure illar da wannan dokar zai yiwa arewacin kasar nan,  wanda kowa ya san da hakan amma shugaban kasa da yan barandarsa sun hakikan ce akan sai an yi dokar wanda zauren majalisar dattijai har tayi karatu na biyu akan shi. Mun zura idanu mu ji karyar da zasu yi bayan sun amshi wannan kwangilar.

Da ya juya kan matsayin jam'iyyar APC kuwa,  cewa yayi jam'iyya ba ta laifi domin tana kundodinta sai dai yayan jam'iyya su ke anfani da son zuciyarsu dan cin ma manufofinsu na boye,  Bola Tinubu dai ya nunawa yan arewa kuma talakawa manufarsa ta boye,  don haka zabi ya rage na su.

Amma tun rantsar da shi muka fahimci irin salon yaudarar da ke zuciyarsa,  duk abinda ya debo akan arewa yake karewa.

Yanzu kuma zabi ya ragewa mai hakar rijiya,  ko ya shiga da matakala ko ya auka gaba daya lokaci na zuwa da zai bayyana mana irin abinda ya shuka mana shi da yan kazaginsa na majalisar tarayya.

Ba yadda za a yi arewa da kamfanoninsu suka durkushe ba a tayar da su ba,  ga matsalar tsaro da yaki ci yaki cinyewa,  ana kwasar mutane a gidajensu ace zasu anfana da wannan sabon dokar haraji da ake son kakabawa yan Nijeriya ba.

Saboda haka,  ina kara jadaddawa talakawan arewa cewar su bude idonsu da kyau,  idan lokaci yayi kar wani ya yaudare su da kudi ko dadin baki su yi abinda ya dace.

Amma ba zamu lamunci gasa aya a kunba ba,  sannan ace za a raba mana kankara dan wanke hannuwan mu ba. Ya kamata yadda gwamnan Barno ya fito ya nuna rashin amincewarsa kan wannan kudurin dokar sauran gwamnoni su fito su goya masa baya tare da lurar da yan majalisun tarayyar da suka fito daga jahohin su kan illar wannan kudurin dokar ga jama'ar su,  hakan zai nunawa talakawan arewa cewar gwamnoninsu na tare da su. 

No comments