Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar APC Fulbe Support Organization ( Bago Ruga Ruga) ta yabawa babban manomin jiha gwamna Umar ...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kungiyar APC Fulbe Support Organization ( Bago Ruga Ruga) ta yabawa babban manomin jiha gwamna Umar Bago bisa kirkirar ma'aikatar jin dadin makiyaya da manoma a jihar Neja, wanda kuma bafillatani ke jagorantar ma'aikatar Kodinetan kungiyar, Alhaji Hassan Usman Shiroro ( Garkuwan Wuro Maliki kuma Wakilin Fulanin Minna) ne yayi yabon lokacin da yake tsokaci kan shirin gwamnatin jiha na samar da kididdigar makiyaya da dabbobin su da aka fara gudanarwa littinin din makon nan a yankunan kananan hukumomi goma sha hudu a matsayin kashin farko.
Wakilin Fulanin ya cigaba da cewar lokacin da gwamna Umar Bago ke yakin neman zube ya tabbatar mana idan ya kafa gwamnati zai samar da abubuwan more rayuwa GA fulanin jihar nan, bayan kammala zube da samun nasara kuma an kafa wannan ma'aikatar wanda Hon. Umar Ahmed Rebe ke kwamishinan ya. Bayan nan gwamna ya ba mukaman siyasa (Political Appointment) guda tamanin da biyu, sannan gwamnatin Bago ta ba mu ma'aikata guda dari, yanzu haka cikakkun ma'aikata ne na gwamnati.
Gwamna Bago, ya yi muna alkawalin ba mu tallafin ilimi ga yayan fulani dan tura su karatu akan kimiyya, wanda kudurin gwamnatin shi ne baiwa yayan fulani damar zama matuka jirgin sama, jirgin kasa da samar da likitoci, wanda yanzu haka muna kan tattara takardun yaran da suka cancanta dan mikawa maigirma gwamna.
Saboda samun nasarorin da wannan ma'aikatar ta samu, yasa gwamnatin tarayya yin koyi da gwamnatin jiha wajen kirkiro ma'aikatar kula da kiwon dabbobi a bangaren tarayya.
Bayan wannan gwamnatin jiha, ta sanya rana ta musamman a matsayin ranar makiyaya dan tunawa da kafuwar wannan ma'aikatar.
Shiroro, ya cigaba da tsokaci akan kididdigar da aka fara, yace alfanu shi, shi yadda gwamnati za ta san adadin makiyaya da ke zaune a kowani bangare na jihar nan da kuma sanin adadin dabbobin da suka mallaka, ta yadda idan gwamnati ta tashi bada tallafi da kuma samar da abubuwan more rayuwa ga makiyayan ta san irin matsaloli da bukatun kowani bangare.
Hakan kuma zai taimaka gaya wajen gano bakin makiyayan da ke shigowa da sanin inda suka fito, tare da tabbatar da tsaro da kuma samun kudaden shiga ga gwamnatin wajen biyan jangali da wasu hanyoyin samun kudaden shiga ga gwamnatin.
Lokacin da maigirma gwamna ya hau karagar mulkin jihar nan, bisa kididdiga muna da makarantun Nomadic guda tamanin da bakwai a dukkanin bangarorin jihar nan guda uku amma ba mu da rayayyar makarantar Nomadic da yayan makiyaya zasu yi karatu. Idan ka dubi shirye shiryen gwamnatin dole ne sai an binciki matsala da dalilin faruwarsa kafin a magance shi, wannan kididdigar daukar bayanan zai taimaka wajen gano bakin zaren da zai baiwa gwamnatin kwarin guiwar magance su, ta haka za a san inda makarantun suke da kuma irin gudunmawar da gwamnatin za ta bayar wajen farfado da su.
Saboda haka, a irin wannan tafiyar dole ne mu hada karfi da karfe wajen kawo karshen koke koken makiyaya da muka dade muna neman mafita.
Ba maganar kungiya ba ce, ba maganar kasar da na ke sarauta ba ne, magana ce ta abinda ya shafi jinsin fulani baki daya. Dan haka na yabawa maigirma kwamishina, Hon. Umar Ahmed Rebe bisa wannan tafiyar da yake yi na babu bambancin kabila, shiyya da son kai, muna kyautata fatar kamar yadda a cikin watanni sha daya aka samu gagarumin nasara da ya zama na biyar cikin kwamishinonin jihar Neja, nan gaba kadan zai zama na farko a kwazo da bajintar aiki.
Garkuwan Wuro Maliki, ya nemi al'ummar jihar Neja, da su zamo tsintsiya madaurin ki daya wajen hadin kai da baiwa gwamnati goyon baya.
Sannan ya kara da cewar wajibi ne mu al'ummar fulani mu baiwa wannan shirin tattara bayanan goyon baya, zai zama mai alfanu gare mu, kamar yadda muka ga gwamna Umaru Bago ya kamo hanya.
Muna bukatar asibitoci a yankunan karkaru, muna bukatar makiyaya dan kaucewa tashin tashina tsakanin mu da yan uwan mu manoma, dukkan su ba za su samu ba dole sai mun baiwa shirye shiryen gwamnatin goyon baya.
Sauran al'ummar jiha su fahimta fulani mutanen kirki ne, amma dole ko a cikin wake akwai lalatacce, sai mun hada kai mun aminta da juna mun zauna lafiya sannan za a samu cigaba. Adalin gwamna, babban manomin jiha, katafila sarkin aiki yana bukatar hadin kan kowa a jihar nan dan samun nasarar da muke nema.
No comments