Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

ABU Ta Sanya Wa Babban Ɗakin Taronta Sunan Marigayi Dakta Yusuf Bala Usman Don Girmama Shi

Daga Bello Hamza, Abuja Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello a taronta na 205 da ta gudanar daga ranakun 4 zuwa 6 ga watan ...

Daga Bello Hamza, Abuja

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello a taronta na 205 da ta gudanar daga ranakun 4 zuwa 6 ga watan Disamba, 2024, ta amince da tunawa da rasuwar Marigayi Dakta Yusufu Bala Usman, Marigayi Farfesa Abdullahi Mahadi, da kuma Marigayi Farfesa Ezzeldin Mukhtar Abdulrahman don karrama su bisa irin gagarumar gudunmawar da suka bayarwa wajen ci gaban Jami’ar Ahmadu Bello da ma kasa baki daya ta hanyar sanya sunayensu a wasu muhimman wurare da ke jami'ar.

Tunawa da rasuwar waɗannan fitattun mutane ya biyo bayan shawarar da mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Kabir Bala ya bayar na karrama su.
Dakta Yusufu Bala Usman, ya kasance ƙwararren malami, haziƙi, dan gwagwarmayar siyasa kuma tsohon shugaban sashen tsangayan tarihi kuma mai son ci gaban ƙasa da ma Afirka, wayayye wajen tsara manufofi. Ya bayar da gudummawa sosai wajen ciyar da tsohuwar tsangayan ilimin sanin kimiyyar sanin zamantakewa, musamman a ɗaukacin jami'o'in ƙasar nan da kuma shahara a ƙasa da ƙasa.

Ya kasance ƙwararre wajen bayar da shawarwari wanda shawarwarinsa suka ba da gudunmawa tare da ci gaba da bayar da gudummawar a jami'a da kasa baki ɗaya.

No comments