Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar Huffazul Qur'an and Islamic Scholars reshen jihar Neja, ta yabawa hukumar da ke kula da tsara jaraba...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kungiyar Huffazul Qur'an and Islamic Scholars reshen jihar Neja, ta yabawa hukumar da ke kula da tsara jarabawar makarantun Islamiyya ( NBAIS) ta kasa da hadin guiwar (FLAILAS) bisa hadin guiwar horar da malaman makarantun tsangaya a jihar Neja.
Shugaban kungiyar, Sheikh Hussaini Abubakar Shakwata ne yayi yabon a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna.
Sheikh Hussaini Shakwata, ya cigaba da cewar wannan shirin mai anfani ne ga malaman tsangaya, domin duk ilimin da malami yake da shi, muddin bai da shaidar karatu ba a daukarsa da muhimmanci, yanzu muna sa ran daukar horo ne na kwanaki goma wanda takardar shaidar da za a baiwa Malami yana matsayin shaidar Grade II ne, ka ga wannan abin a yaba ne.
Shugaban ya kara da cewar ba nan gizo ke sakar ba, domin yau ba abinda za ka fuskanta ka samu nasara sai da kudi, kuma kungiyar nan jaririya ce ba mu da wani asusun da za mu dauko mu bayar, tun fara wannan horarwar a kulli yaumin a cikin aljihuna ina kashe a kallan naira dubu hamsin, da gwamnati za ta taimaka ko wasu masu hannu da shuni da mun yi farin ciki da hakan.
Wannan nauyi ne da ya rataya akan gwamnati amma wata hukuma ta dauki nauyin shi, dan haka muna kira ga gwamnatin jiha da hukumar kula da ilimi na jiha da su taimaka dan ganin shirin bai tsaya ba, musamman ganin NBAIS tayi muna alkawalin cigaba da wannan horarwar har zuwa matakin digiri.
Yanzu haka muna da alarammomi guda saba'in daga jihar Neja da ke halartar wannan horaswar, kuma muna fatar kamar yadda wannan hukumar da hadin guiwar makarantar FLAILAS suka ba mu wannan damar hakan zai taimaka wajen karfafa guiwar gwamnati wajen baiwa Alarammomin Al-kur'anin mai tsalki daman damawa da su a harkokin gwamnati, musamman wajen bada ayyuka da duk wani abinda ya shafi bangaren makarantun tsangayu da harkokin yau da kullum na gwamnati.
Shugaban yace damar manufar kungiyar Huffazul Qur'an, shi ne samar da dama wajen hadin kan malaman tsangaya musamman a yunkurin gwamnati na kawo mafita ga yawan barace barace ga kananan yara da sunan karatun allo, wanda assasa wannan tafiyar ya taimaka gaya wajen wayar da kan malaman tsangaya manufofin gwamnati da kuma baiwa gwamnatin shawarwarin hanyoyin da ya kamata a bi wajen cin ma kudurce kudurcen gwamnatin.
Shakwata, yace ina baiwa mambobin kungiyar nan kwarin guiwa duk lokacin da gwamnati ko wata kungiya mai zaman kan ta, ko wata hukuma suka bullo da wasu abubuwan cigaba za mu tsaya kai da fata wajen ganin mambobin mu sun anfana .
No comments