Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Malaman Tsangaya Sun Nuna Takaicinsu Kan Yadda Wasu Makusantan Gwamna Bago Ke Yunkurin Goga Masa Bakin Jini

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar mutuwar babban Limamin Minna,  Malam Ibrahim Isah Fari, babban rashi ne da ba za a iya mantawa da...



Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar mutuwar babban Limamin Minna,  Malam Ibrahim Isah Fari, babban rashi ne da ba za a iya mantawa da shi ba.  Mataimakin shugaban kungiyar Mahaddata da malaman tsangaya reshen Arewa ta tsakiya,  Amb. Musa Adamu ne ya bayyana hakan kan wata badakalar da suke zargin wasu makusantan gwamna Umar Bago da yi masu lokacin gudanar da taron addu'o'in da malaman suka gudanar,  wanda a cewarshi duk lokacin da aka shirya irin wannan taron ko gwamna ya samu halarta ko bai samu ba, akwai sako na musamman da gwamna kan bayar wanda marigayi Malam Ibrahim Isah Fari sai ya tabbatar dukkanin kungiyoyin addini da suka halarta sun samu kason su.

Amma abin bakin ciki da ya janyo kananan maganganu ko yanzu,  akwai zargin gwamna ya bada sakon wasu ne ke kokarin dannewa.

Ba mu taba shirya wani taron addini ko yin addu'o'in zaman lafiya ga kasa,  tun zuwan gwamna Umar Bago kan mulki ba mu ga tallafinsa ko gudummawarsa ba,  amma kasa da watanni biyu da rashin uba kuma babban limamin Minna,  abubuwa sun fara canjawa,  saboda haka ina jawo hankalin wadanda gwamna ya aminta da su da su ji tsoron Allah,  idan suna wannan abin bisa kuskure ne to su daina,  muna da hanyar duk da za mu bi wajen haduwa da gwamna,  amma ba dabi'armu ba ne wannan.

Mu masu biyayya ne da kuma goyon bayan wannan gwamnatin dan haka ne a kowani lokaci muke yiwa gwamna Umar Bago addu'o'in samun nasara, musamman duba da irin ayyukan cigaban kasa da fitar da jihar Neja kunya wajen samar da sabuwar jihar Neja.

Amb. Musa Adamu,  ya nemi malaman tsangaya,  da almajirai kamar yadda suke baiwa gwamnatin nan goyon baya da addu'o'in samun nasara,  kar su ja baya,  amma a kowani lokaci wasu suka aiwatar da abubuwan da ba daidai ba,  akan kudurin gwamnatin jiha na cigaba za mu fito mu fada domin jama'a muke jagoranta su san abinda ke faruwa.

Tun ba aje da nisa ba,  mun fara kewar rashin Malam Ibrahim Isah Fari,  to inda ya tafi da daidai zamu cin masa,  yau adalcinshi ake fada bayan ba rayywarsa,  su ma wadannan makusantan gwamna wadanda gwamna ke baiwa amanar al'umma su yi mirsisi,  Allah ya ba su ikon gyarawa,  sannan su sani wannan ba zai sa mu janye goyon bayan ga gwamna Umar Bago ba,  kuma dukkanin addu'o'in da muka iya na samun nasarar wannan gwamnatin za mu cigaba da aiwatarwa,  jihar nan idan ta cigaba kuma gwamnatin nan ta samu nasara mu ne za mu anfana gaba daya. 

No comments