Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da ƙudirin kasafin kuɗin shekarar ...
Akpabio ya bayyana hakan ne a majalisar ranar Alhamis a cikin zauren Majalisar Dattawa.
Ya ce, “Shugaban Ƙasa ya bayyana aniyarsa ga majalisar dokoki ta ƙasar na gabatar da kasafin kuɗin 2025 a zaman haɗin gwiwa na Majalisar a ranar 17 ga Disamba, 2024.
Akpabio ya bayyana cewa za a gabatar da kasafin ne a Zauren Majalisar Wakilai.
Tunda farko Tinubu ya gabatar da daftarin tsarin kashe kuɗi matsakaici na 2025-2027 ga Majalisar Dattawa da ta Wakilai a ranar Talatar da ta gabata.
Akpabio ya umarci kwamitin Majalisar Dattijai mai kula da harkokin kuɗi, tsare-tsare da tattalin arziki da ya duba takardun tare da bayar da rahoto cikin mako guda.
No comments