Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CBN Ta Tabbatar Da Ingancin Tsoffin Kudi Na Naira 200, 500 Da Kuma 1000

Babban Bankin Nijeriya, CBN ya nanata ingancin tsofaffin takardun kuÉ—in Nijeriya na naira 1000, 500, da kuma 200. Ya bayyana hakan ne a wata...


Babban Bankin Nijeriya, CBN ya nanata ingancin tsofaffin takardun kuÉ—in Nijeriya na naira 1000, 500, da kuma 200.

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a dauke da sa hannun Hakama Sidi Ali, Daraktar yada labarai da hulda da jama'a na bankin.

Babban bankin Nijeriyar ya ce ya lura da labarai karya da ake yadawa akan lamarin, inda CBN ta jaddada cewa tun bayan hukuncin da kotun koli na Nijeriya ya yanke dangane da ingancin tsoffin kudin Nijeriya, har yanzu tsoffin kudin ingantattu ne.

Bankin har wala yau ya ce kowa ya cire shakku, domin dukkanin wani nau'in naira na Nijeriya wanda ya hada da tsoffi da sabbin da aka fitar; baki dayan su ingantattu ne.

A don haka sun yi kira ga al'umma da su yi watsi da duk wata jita-jita da labarai dake nuni da cewa an daina karbar tsoffin naira 200, 500 da kuma 1000. 


No comments