Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sakataren Gwamnatin Bauchi Ya Yi Murabus

A ranar Juma’a ne Sakataren gwamnatin jihar Bauchi (SSG), Barista Ibrahim Muhammad Kashim ya ajiye aikinsa bisa dalilan da ba su bayyana ga ...



A ranar Juma’a ne Sakataren gwamnatin jihar Bauchi (SSG), Barista Ibrahim Muhammad Kashim ya ajiye aikinsa bisa dalilan da ba su bayyana ga jama’a ba zuwa yanzu. 

Sakataren ya ajiye aikin ne a wata wasiƙa da ya aike kai tsaye wa gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad.

Tuni dai gwamna Bala Muhammad ya amince da ajiye aikin sakataren gwamnatin nasa tare da masa fatan alkairi a rayuwarsa ta gaba.

Gwamnan a wata sanarwar da kakakinsa, Mukhtar Gidado ya fitar da yammacin ranar Juma’a, ya ce, ya amince da murabus É—in Ibrahim Muhammad Kashim a matsayin SSG nan take.

Gwamnan ya umarci shugaban ma’aikatar fadar gwamnatin jihar, Dakta Aminu Hassan Gamawa da ya ci gaba da kula da harkokin ofishin SSG na riÆ™on Æ™warya kafin a naÉ—a sabo.

“A madadin gwamnatin jihar Bauchi da al’ummar jihar, ina matuÆ™ar godiya ga Ibrahim Muhammad Kashim bisa hidimar da ya yi wajen ci gaban jihar Bauchi. Ina masa fatan alkairi a rayuwarsa ta gaba,” a cewar sanarwar.

LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, har yanzu dai ba a san dalilan da suka sanya SSG ɗin ajiye muƙaminsa ba wanda ke zuwa bayan taron gaggawa na majalisar zartarwar jihar da ya gudana a ranar Alhamis.

No comments