Daga Awwal Umar Kontagora Mai martaba sarkin Minna, Dr. Umar Faruq Bahaga ya kawo karshen rikicin shugabancin kungiy...
Daga Awwal Umar Kontagora
Mai martaba sarkin Minna, Dr. Umar Faruq Bahaga ya kawo karshen rikicin shugabancin kungiyar Markazul Qur'an ta kasa, sakamakon rikicin shugabanci tsakanin Gwani Sanusi Abubakar da Sheikh Hassan Musa.
Takaddamar shugabancin ya biyo bayan zabukan da aka gudanar na farko a jihar Bauchi da ya baiwa Gwani Sanusi Abubakar nasara da kuma zaben da aka gudanar a jihar Sokoto wanda ya baiwa Sheikh Hassan Musa nasara kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Tunda farko da yake jawabi bayan kammala zaman, Gwani Sanusi Abubakar ya yabawa mai martaba sarkin Minna bisa rawar da ya taka na kawo karshen takaddamar shugabancin, yace wannan sulhun alheri ne kuma shi zai kawo hadin kai tsakanin shugabannin Markaz da mambobinta.
Saboda mun yabawa fadar mai martaba da shi kan shi mai martaba bisa namijin kokarin samar mana da maslaha, wanda shi kan shi jagoran wancan bangaren Sheikh Hassan Musa ya nuna jarunta kuma akwai bukatar mu hada kai dan cigaban tafiyar baki daya.
Shugaban, ya kuma yabawa Sheikh Hussaini Abubakar Shakwata, shugaban kungiyar Huffazul Qur'an and Islamic Scholars ta jihar Neja, bisa jarunta da kokarin da suka taka na samun wannan maslahan da muke kyautata zaton zai kawo mana karshen rarrabuwan kawuna.
Da yake tsokaci ga wakilin mu, Sheikh Hassan Musa, shugaban kungiyar Markaz ta kasa na farko, yace ya janye takaddamar duk da cewar ba shi ne ya zabi kan sa ba.
Hassan Musa, yace mai martaba sarkin Minna, uba ne kuma wanda dole ayi biyayya ga umurninsa, kamar yadda mai martaba yace zaman lafiya, hadin kai da yiwa kasa fatar zaman lafiya yana da muhimmanci koda kana da gaskiya idan manya sun baka umurni ka yi biyayya.
Dan haka muna jawo kan hankalin mabiya da masoya da kowa yayi hakuri mu rungumi juna, kuma a shirye muke wajen samar da duk wani abinda zai kawo tsangayun Alqur'ani mai tsalki mai martaba tare da tabbatar kare martaba da mutuncin almajiran tsangayu.
Hassan Musa, yace daman babu fada tsakanin mu da su Malam Sanusi, domin na yi aiki da shi lokacin muna da kyakkyawar fahimta a matsayin sakatare na lokacin ina shugabantar Markaz, saboda mun bi sulhu domin sulhu alheri ne.
Takaddamar ta dauki tsawon lokaci ana fafatawa, wanda a yammacin juma'ar nan mai martaba sarkin Minna, ya jagoranci sulhun inda dukkanin bangarorin suka sanya hannu na zaman lafiya, bayan ganawarsu da jami'an tsaro. A yanzu dai Gwani Sanusi Abubakar shi ne halastaccen shugaban Marzakal Qur'an ta ka wata Centre for Qur'anic Recitation, inda Sheikh Hassan Musa ya amince da janye ikirarin bangarancin sa a rubuce.
No comments